Labaran yau da kullum

Yanda Wani Aboki ya yi ma Dogarin Sarkin Saudiya Mummunan Kisa

Gidan talabijin din Kasar Saudiya ya tabbatar muna da kisan da an ka yi ma wani babban mutum wato babban dogarin Sarki Salman Maj. Gen Abdulaziz Al-fagham wanda sun ka ce an halbe shi har lahira, kisan cin amana. Maj. Al-fagham dai ya gamu da mutuwar shi ne a lokacin da ya kai ma abokin shi Faisal Bin Abdulaziz al-sabti ziyara a Birnin Jedda amman kuma sai ga wani abokin shi da ake kira da Mamdou Bin Mishal Al-ali yazo wurin inda bada jimawa ba an ka ji shi da General Al-fagham sun fara gardama inda nan take an ka ga Al-ali ya koma gida ya dauko bindiga nan take ya bude ma General din wuta tareda shi da wasu mutane biyu dake wurin da kuma maigidan Turki Al-sabti.

Read also  Wani Dan Jamhoriyar Nijar yazo na ukku a Gasar karatun Alkur'ani ta duniya

Yansanda dai sunyi kokarin kawo dauki amman nan take su ma Al-ali ya bude masu wuta inda sun ka yi nasarar halakashi lokacin da sun ka maida wuta. An dai yi kokarin kai su Al-Fagham assibiti amman bada jimawa ba Allah ya karbi rayuwar Maj. Al-fagham amman sauran mutane suna da sauran kwana gaba inda yanzu likitoci na basu kulawa yansanda kuma suna cigaba da bincike.

Muma munce Allah ya jikan shi. Ya kuma tsare gaba

Hassan Haruna Gobir

Hassan Haruna Gobir, from Sabon Birni in Sokoto State, is GobirMob.com publisher and writer. He primarily focused on Nigeran politics, Gobir News and Sports.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Close
Close
WhatsApp Join Group