Kundin Kannywood

Duk wanda kaga ya lalace to lalatacce ne tun daga Gidansu – Jarumi Sadiq Sani Sadiq

Fitaccen jarumin Kannywood Sadiq Sani Sadiq ya ce kwarewarshi ta iya taka kowace rawa ce ta sa ya lashe gasar jarumin jarumai sau ukku a jere.

“Idan har Ina cikin Kannywood ni ne zan ci gaba da lashe gasar jarumin jarumai a kowace shekara saboda bani wasa da aikina”, in ji Sadiq Sani Sadiq, a tattaunawa ta musamman da BBC Hausa.

Ya musanta zargin da ake yi cewa yana jajircewa a Hausa film ne domin ya dusashe taurarin jarumai Ali Nuhu da Adam A Zango, yana mai cewa “su iyayen gidana ne domin kuwa sun taimaka min sosai a wannan harkar. Ka ga kuwa babu wanda zai ja da iyayen dakinshi.”

A cewarshi, “Ni ina yin shiri ne a matsayina na Sadiq Sani Sadiq, kuma ina da kwazo, da jajircewa, da maida hankali sosai a kan aikina, shi yassa nake ganin babu wata gasa da za’a yi da ba zan lashe ba.”

Read also  Jarumar Kannywood, Fati Shu'umah tace bata ce tana son Shugaba Buhari da aure ba

Sadiq Sani Sadiq, wanda ake yima lakabi da Dan marayan zaki, ya kara da cewa yana son danshi ya gaje shi.

Jarumin ya ce a baya ya yi kiwon karnuka sosai shi yassa “da aka sa ni a wani shiri a matsayin mafarauci ban fuskanci wata matsala ba”.

“Abun da ya sa nake iya taka ko wace rawa shi ne, na yi hulda da mutane dabam-dabam a rayuwa tun ma kamin na shiga harkar Kannywood. Shi yassa idan aka sa ni a matsayin mai saida shayi, misali, za ka ga na yi abun tamkar mai shayin gaske saboda na taba yin hulda da su,” in ji jarumin.

Read also  Jarumar Kannywood, Maryam Booth zata yi aure

Sadiq Sani Sadiq ya bayyana zargin da ake yi ma ‘yan Hausa film na neman maza da cewa “karya ce kawai. Ni ban taba ji ko ganin wanda yake luwadi ba. Kuma na dade Ina yin wannan masana’antar. Ka ga kuwa tun da haka ne sai kawai in ce karya da kazafi ake muna.”

Ƙarahe yace ba aikin ‘yan film ne koyar da mutane tarbiya ba kamar yamda wasu ke hasashe, yana mai cewa, “Duk wanda ya ce ‘yan film sun bata mashi tarbiyya da ma ba shi da ita. Ai tun daga gida ake samun tarbiyya”.

Malik al-Ashtar

Ashtar Hamisu from Birnin Maradi, Niger Republic, is Nigeriene Blogger and Chief editor at GobirMob.com. He writes bilingually on Niger News and Entertainment.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Close
Close
WhatsApp Join Group