Labaran yau da kullum

Wata tsinuwa duk Dan Wasan da yayi hoto da Mawaki Drake sai yayi rashin Nasara

A kwanan nan kungiyar kwallon kafa ta As Roma ta haramtama yan wasanta daukar hoto da mawakin nan kasar America Drake wanda a yan kwanakin nan duk wanda yayi hoto dashi sai yayi rashin nasara,inda a baya-bayan nan dan wasan kungiyar PSG Layvin Kurzawa yayi hoto dashi sai gashi Lille ta lallasa su da ci 5 – 1. hakazakima shima Paul Pogba sai gashi Wolves ta lallasa Manchester da ci 2 – 1 haka shima dan wasan gaban Arsenal sai gashi Everton taci 1 da nema sai kuma Kun Aguero da barar da fanareti sannan kuma Tottenham taci 1 – 0 a wasan zakarun turai. Haka ma matashin dan wasan England dake taka leda a Bvb Dortmund bai tsiraba inda shima Bayern Munich taci su 5 -1.

Read also  Hotuna: Ana raɗe-raɗin cewa Diyar Shugaban Kasa Zahra Indimi na ɗauke da Ciki

Wani karin rashin sa’a ma hatta dan wasan damben nan na UFC Conor Mcgregor a shekarar data gabata da yayi hoto dashi sai gashi Khabib Numagomedov ya hambarar dashi tun a zagaye na hudu. Akan haka yanzu kowane dan wasa yake shakkun daukar hoto da Drake don kamar hakan wata tsinuwa yake janyowa.

Hassan Haruna Gobir

Hassan Haruna Gobir, from Sabon Birni in Sokoto State, is GobirMob.com publisher and writer. He primarily focused on Nigeran politics, Gobir News and Sports.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Close
Close
WhatsApp Join Group