Videos

[Video] Mawaki Mamman Sagalo ya na wake Yan Kokowar Niger a wata shekara

Alhaji Mamman Sagalo sanannen Mawaki ne daga Jamhoriyar Nijar, wanda ya shahara a hwagen Wakoki na Kokowa, shi ne ke wake Yan Kokowar Niger a kowace shekara idan ta tashi.

Sagalo tareda yan amshin shi su na waken su ne na ƙara ma Yan Kokowa a hwage kwarin guiwa ta hanyar kirara su da yabon su. Wagga wakar ta dubu biyu da shatakwas ce. Cikin ta mun ji yana kirara su Bindigau da Natabawa da Kadade da sauran su.

Amman kwanan baya naji wasu su na cewa Allah ya yi ma Alhaji Mamman Sagalo cikawa, wato ya rigya mu gidan gaskiya, ya mutu. Ba mu sani ba ko da gaske su ke ko shaci hwaɗi ne.

DanZubair

I am Abdul-Raheem Zubair by name, Founder- Operator at GobirMob.com. My hobbies are reading, travelling and discovering.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

WhatsApp Join Group