Kundin tarihi

Tuna baya: Kun ga Hotunan Garin Maradi na shekara 100

Abun mamaki an bayyana hotunan Birnin Maradi tun tana matsayin ƙauye yau wajen shekaru ɗari ɗaya (100) da sun ka gabata tun 1920, kamar yanda alƙaluma sun ka bada. Hoton ya fito ne daga ma’adana kayan tarihi na Birnin Maradi wanda ya kamanta zamanin da take matsayin ƙauye, wataƙila an bayyana shi ne ko dan tunowa da cikarta shekara ɗari (100) da zaman turawan mulkin mallaka a yankin daga gani.

A bisan hoton an bayyana rubutun sunan “Niger”, a ƙasa sai an ka sa rubutu “Un Village du Niger, Maradi”, wato, Ƙauyen Nijar, Maradi. Sauran rubutun dake tsakkiya bamu gano shi ba saboda ya dusashe sakamakon daɗewa da guga da kayan ajiya ko sanadiyar ruwa sun taɓa launin rubutun.

Hoton ya bayyana mutane, wasu mata su huɗu ɗauke da ƙumussa ko tuluna ne a kai zasu tafi kasuwa dan saye da saidawa ko rijiya dan ɗauko ruwan sha. Sannan sai ga akuya nan raɓe da su, ko ita ce irin wannan akuyar ta Maradi wadda babu irinta. Zagaye dasu ga itatuwa nan alamun daji, sai kutuɓɓa da darnakku, sai sararin samaniya.

Akwai makeken rame nan gaban hoton kamar tabkin da ya ƙwafe. Tarihin Maradi Jiya da Yau.

DanZubair

I am Abdul-Raheem Zubair by name, Founder- Operator at GobirMob.com. My hobbies are reading, travelling and discovering.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

WhatsApp Join Group