Tarihin daɗaɗɗar Masarautar Gobir da jerin sunayen Biranen

0

Tarihin Gobir ya faro tun shekaru 5,000 da tashi ko hijira na tsawon shekara 1,100. Ta bakin bayanin da shugaban “Maradi Institute for Social Sciences” IRSH, Malam Sani Habou Magagi, In muka dauki tarihin tun daga Gabas ta tsakkiya, Gobirawa sun taso daga Baghdad. Kenan kasar Iraq ta yanzu, wanda can ne mazamninsu na farko ko birni. Mazamninsu na biyu ko birni shine Birnin Qudus a Jerusalem, Birninsu na ukku shine Birnin Gubur a Yamen inda sunka samo sunan “Gobir”, Na hudu shine Birnin Karbala cikin Saudi Arabiya, Na biyar shine Birnin Masar (Egypt cikin Afruka). Birni na shidda kuma shine Birnin Surukan cikin Tunisiya, Na bakwai shine Birnin Tunasse shima duk cikin Tunisiya (Afruka ta Arewa), Birni na takwas shine Birnin Bagazam (wanda yanzu Abzinawa ke kira Agadez yanzu) a Jamhoriyar Niger cikin Afruka ta Yamma, Na tara shine Birnin Aigadasse shima cikin Jamhoriyar ta Nijar, Na Goma shine Birnin Tinliguilit a Nijar shi ma, Na sha-daya shine Birnin Marandat a Nijar, Na sha-biyu shine Birnin Toro a cikin Nijar, Na sha-ukku a Birnin Lalle cikin Nijar, Na sha-hudu shine Birnin Gwararabe cikin Nijar, Na sha-biyar shine a Birnin Alkalawa cikin Nijeriya, Birni na sha-shidda shine Birnin Dakwarawa cikin Nijar, Na sha-bakwai shine a Birnin Gawon Gazau cikin Nijeriya.

Birnin na sha-tawas shine Birnin Maradi cikin Jamhoriyar Nijar (bayan biyawa ta sada zumunci da danginsu Katsinawa) sannan sai na sha-tara kuma na karshe wato Birnin Tibirin Gobir a Nijar. Kenan biranen su sha-tara ne, daga Iraqi zuwa Nijar, cikin hijra ta tsawon shekara 1,100; Kuma cikin waɗannan tsawo hijirar, Gobirawa na farko sun yi auratayya da ƙabilun da sunka tarar a tafiyar.

Ta bakin bayanin da shugaban na IRSH ya bada, Birnin Tibiri (Gobir) an kafashine a cikin ƙarni na 19, wato a shekarar 1835 ga Sarki Gobir Djibon Taouba; Gobirawa sun kafa birninsu na sha-tara Birnin Tibiri a 1835, ƙarshen yaƙin Dakwarawa tsakanin Sultan Muhammadu Bello (Sarkin Sakkwato na biyu bayan Usman Danfodio ubanshi) da sarakuna: daya na Katsina Maradi, mai suna Sarki Raouda da gudan na Tibiri wanda ake cema Sarki Ali.

Ta bakin Sani Habou Magagi, In munka ɗauki cikin jerin sarakunansu kamo daga sarki na farko zuwa na yanzu, na 380 cikin Sarakunan na Gobir, Sultan El hadj Abdourahmane Balla Marafa, zamu iya cewa Gobir ta yi gagarumin tashe zamanin Sarkin Gobir Bawa Jangwarzo. Jarumtakarshi ta kai bango hudu na duniya. Cikin zamani nai babu mai wata ƙeta sannan kuma shine uba ga Gobirawa. Ya roƙi Allah ya bashi mu’uzija da babu irinta wadda ita ta sa ya zama sanannen jarumi har waje ga Gobir a zamanin. Abubuwanda ya jawo ci baya ga masarautu ko daulolin Afruka ta Yamma shine “Jahadi” na El Hadj Omar a Sudan ta Yamma, sai na Usmanu Danfodio a Tsakkiyar Sudan da “Jahadi” na Mahadi a Sudan ta Gabas. Kuma cikin wannan lokacin ne, ƙarni na 19, aka yi waɗannan Jahadodin su ukku. Maganar abubuwanda suka jawo ci bayan Gobir, akwai Yakin Fulani na Usman Danfodio wanda ya tadda rikici tsakanin Sarki Yunfa da Ƴan uwanai; Akwai kuma ƙananan yaƙoƙi na ƙabilanci tsakankanin wasu masarautun hausa sai kuma a shigar ƙarni na 20 inda turawan mulkin mallaka sunka kutso wanda ya ƙara taimakawa ga raunana waɗannan gawurtattun masarautu na Afruka.

Leave A Reply

Your email address will not be published.