Tarihin Birnin Lalle da sarkinta na mutum-mutumi, Sarki Kututturu

0

Akwai wata masarauta daga cikin daɗaɗɗun masarautun Afrika, wani gari mai suna Birnin lalle dake cikin yankin Dakoro a Jahar Maradi, Jamhoriyar Nijar. Tsohuwar Masarautar Gobir ɗin tayi suna ne a tarihin Gobir saboda abubuwan tarihin da sunka wakana a cikinta: Birnin itatuwan lalle (itatuwan da sunka samarwa garin sunanshi) wanda yanzu babu yawancin su a tabkin saboda kolliyar jiki da matan hausawa ke yi da lalle, wankan lalle lokacin aure da sauransu; Kushewar Tahoua, mazamnar kabarin sarauniyar mata ta farko da aka yi a Gobir wato Sarauniya Tahawwa, uwa ga wanda suka kafa Birnin konni dake cikin Jahar Tahoua a Jamhoriyar Nijar da Masarautar Argungu a jahar Kebbi, Nijeriya; Masarautar da Sarki Dalla Gungume yayi mulki, ana kuma kiranshi da Sarki Kututturu (ɗaya daga abubuwan tarihin ban mamaki da aka taɓa yi a Afrika); mazamnar tabkin tarihin da babu irinshi a kasar, “Tabkin lalle”, wanda yake janyo ƴan yawon buɗa ido daga ciki da wajen Jahar Maradi, Jamhoriyar Nijar.

Birnin lalle shine birni na gaba bayan Gobirawa sun baro Birnin Marandat da Birnin Toro. Sun kafa birnin ɗaruruwan shekaru da sunka gabata sanda suke neman ma’adanar ruwa, gulbi ko tabki wanda zasu rinƙa ayukkansu na noma, kasancewarsu manoma tun farkon-farko. Birnin ya samo sunanshi ne daga itatuwan lalle da sunka tarar a gaɓar tabkin, da isowarsu wurin da ganin itatuwan nan, nan-da-nan sunka ba garin suna, daga cewa “Wannan wuri Birnin lalle kenan!” Wannan tabkin shine dalilin zamansu nan, saboda daɗaɗɗen aikinsu noma da kuma cewar ruwa sune rayuwa. Ta bakin masana tarihi, Birnin lalle ta kafu tun shekaru 2000 da suka gabata. Gobirawa a zamanin daure matafiyane na ƙwaran da gaske, sun sha ƙaura da tafiya tun daga Baghdad har zuwa mazamninsu na ƙarshe, sannan kuma cikin biranen da sunka baro a baya, kowane nada dalili tattare da tashi dagareshi ko barinshi… “Kwararowar hamada”, “Rashin cimaka”, “Rashin ruwan noma”, “Yaki” da wasu matsaloli na rayuwa, kamar yadda aka bayyana. Amman a ɓangaren Birnin lalle dalilin shine rashin cimaka da ya ɓarke a garin.

Bayan wanda sunka kafa garin sun yi hijira, ance garin ya sake yin wani tashe shekaru 300 da suka gabata a matsayin cibiyar kasuwancin zamanin, ta bakin wani masanin tarihin baka a tsohon garin, inda tarihi ya bada cewa Tawagar ƴan kasuwar Kano basu tsayawa bisa hanya su saida kayansu- doli sai sun iso Lalle, lokacin cibiyar kasuwanci ta yanzu “Maradi” na a matsayin ƙauye ko kuma ba’a kafata ba.

Birnin lalle ta taɓa zama Babban birnin Faransawa ƴan mulkin mallaka a yankin, amman bayan Shugaban yankin ya damu da kukan kwaɗɗin dake fitowa daga tabkin, Maibuje (sunan da mutanen nashi suka laka mai, ma’ana wanda ke sanya buje) ya gusarda birnin zuwa Dakoro ta yanzu, gari mai nisan kilo 15 daga Birnin lalle.

Sarki Issuhou Maidabo shine sarkin daɗaɗɗar Masarautar ta Birnin Lalle. An naɗashi bisa sarautar tun tsawon shekaru 50 da suka wuce da cikakken iko ga ƙauyukka da garuruwan dake ƙarƙashin Masarautar a Gwamnatin Faransawa, wasu garuruwan kuma a ƙarƙashin Masarauta makwabciya, Kornaka dake ƙarƙashin riƙon Abzinawa, amman asalinta da can Masarautar Gobir ce.

Abzinawa sun samu damar hawa mulki a masarautar bayan kakansu Sarki Jaku ya sabka a Garin Kornaka. Ya auri Gimbiya Bagobira mai suna Gimbiya Sahiya. Sanda Sarki Bagobiri da ya mulki masarautar ƙarshe ya rasu kuma baida magadi da zai gadeshi, Jaku ya roƙi surukainai, sarakan Tsibiri Gobir su bashi dama shima ya hau sarauta kuma basu iya cewa a’a dan Gobirawa nada wata tabi’a ta kumyar surukkansu, sai sunka naɗashi. Zuri’atai ce ke mulki a daɗaɗɗen Garin Kornaka dake tattareda jama’ar Hausawa, Abzinawa, Buzaye, Zabarmawa, Barebari da Fulani a yankin na Dakoro, Jahar Maradi a Jamhoriyar Nijar.

Tabkin Lalle ya mamaye kusan eka ɗari a misali, ga shibke-shibken itatuwa iri-iri da ake samu a yankin, sai zazzaƙan kukan tsuntsaye dake tarben mutum sanda ya kama hanyar shiga tabkin. Tabkin tarihin da babu irinshi a Nijar na samun ziyarar yan yawon buda ido daga ciki da wajen kasar, mafi yawancin lokuttan bukukuwan sallah. Ruwan tabkin, a lokacin rani na ba masu noman gandari damar samarwa garuruwa da kauyukkan kewaye kayan danye da ɗiyan itatuwa inda su kuma manoman suke samun kuɗaɗen shiga ta hakan. Ƙarawa da ƙarau, ƙarƙashin shugaban ƙasar mai ci yanzu da sa hannun ƙasashen waje, noman na rani yanzu an ƙarfafa shi da bada injinukkan tsotso ruwa da wayar ma mazamna garin da kai gameda noman rani. Shugaba Muhammadou Issuhou ya fito da wani shiri mai taken “Dan Nijar ya cida Dan Nijar”, manufarshi shine Yan Nijar su yi amfani da noman rani wajen samarwa mutanen kasa kayan abinci a shekarar 2015 kuma Birnin lalle na daga wanda sunka ci gajiyar wannan shirin har wa yau. Tabkin lalle na daɗewa da ruwa dan saboda haka makyayan Rakumai da Shanu, Abzinawa makyaya da Fulani makyaya, na tunkara tai da bisashensu duk sanda ruwa sunka kakare musu a sauran tabkunan kasar.

Sarki Kututturu na daga sarakunan da aka yi a birnin; Sarki Barankame, Sarki Kanni, Sarki Bartakeskes, Sarki Hammadin, Sarki Bartuwatuwa da wasu na daga cikin sarakunan Gobir wanda aka ƙiyasta sun kai su dari ukku da tamanin (380), amman abun ban mamaki shine Sarki Kututturu ba mutum bane- icce ne aka sassaƙa aka naɗa. Sarkin kututturu wata alamace ta azancin Afrikawa da suke bijirowa da ita dan shawo kan matsalolin da sunka addabe su. Wannan na daga abubuwan tarihin da sunka abku a Gobir, kuma ana ƙidaya sarkin cikin sarakunan Gobir.

Dubara ta zo ma sarakin wata rana da suka shiga daji kilisa, sun samu kututturun icce sunka sassaƙo mutum sunka naɗashi sarki. Sun bijiro da wannan dubaran ne dan su dakatarda kashe-kashen da ake ma sarakunan da basu ji basu gani ba a Birnin lalle lokacinda sarakin gobir suka samu rashin jituwa tsakaninsu danganeda zaben sarki. Bayan an yi bikin naɗin Sarki kututturu, sarakin da basu so sun sake yo yunkurin kawarda sarkin, kamar yadda suka ga bayan wasu a baya, amman sun tararda Sarkin dangalgal bisa karagar shi. Ga nasu tunanin basu san adadin layun ko karhunan da ya tanada ba da suka sa bai razana da ganinsu ba ko kuma abunda ke cikin zucciyar shi, daga nan sunka sallama suka bari aka naɗa sarakuna mutane tun kafin su tashi daga garin. Sarki Kanni da Sarki Hammadin ɗiyan da sunka ragema Sarauniya Tahawwa sun tsira da rayuwarsu da suka kama hanyar tsira da dare, kamar yadda suka shawarta. An tilastasu hawa gadon sarautar ɗaya bayan ɗaya cikin basu so. Koda aka naɗa Kanni dare na yi ya hau sirdi ya bace ba’a san inda ya dosa ba. Shi ma kanen kanni, Hammadin da aka naɗa shi shi ma ya bi ɗanuwar shi. Sarki Kanni shine ya kafa Birnin konni cikin Jamhoriyar Nijar, Hammadin kuma bayan ya yi ɗan zama tareda wan nashi yayi ƙaura yaje ya kafa Masarautar Argungu a jahar Kebbi Nijeriya yanzu.

Duk sanda Uwar su Sarauniya Tahawwa ta tuno yadda ɗiyan da suka rage mata suka yi ɓatan dabo sai tace “Gobirawa haka kunka kai ni, bani ga Kanni, bani ga Hammadin?” cikin ɓacin rai, ta bakin baitin mawakin gargajiya kuma masanin tarihi, Margyayi Alhaji Maidaji Sabon Birni.

Bayan wannan ta samu haɗuwa da ɗiyanta biyu bayan an gano inda suke. An kawoma Sarki Kanni matar shi mai ciki wadda ya baro a Birnin Lalle kuma masoya nai suka yo dandazo suka zamna taredashi. Sarki Kanni da kanenshi Sarki Hammadi kowane nada tsagen Gobirawa nan shidda (6) nan bakwai (7) zane a kumatunsu na dama da na hagum, da lokacin haihuwar ɗiyansu na farin suka yanke shawarar kowane ɗa za’a mai tsaga goma (10) da sha-biyu (12) dan su bambamta ɗiyansu daga sauran ɗiyan Gobirawa. Bayan ƴan shekaru da zama da magaji nai Kanni shugaba mai farin jini kuma wanda ya shahara, Hammadin, ganin ya iya tsayawa da kai nai, ya tashi daga nan shi ma yaje ya kafa tashi masarauta, Argungu cikin jahar Kebbi, Nijeriya.

Nasan mutane zasu rinka tambaya ya Sarki Kututturu yayi sha’anin mulkinshi, to Sarki Kututturu nada fadawa da masoya kuma duk sanda mutane suka zo yin gaisuwar fada, fadawan zasu amshe su maida da, “Sarki ya gaisheka”, watakila wannan ne mafarin irin wannan amshin gaisuwa a tsarin Shugabancin Hausawa. Shari’a kuma ko sasanta matsalolin zamantakewar mutane, wakilai ke yin ta a fada inda suke maye gurbin sarkin, duk sanda ake buƙata.

Leave A Reply

Your email address will not be published.