Takaitaccen tarihin Fati Washa da Kyawawan Hotunan ta

8

Fati Washa mai son sana’ar shirin kwaikwayo ce tun tana ƙarama. Kasancewarta mai taimakama jarumai bai durkushe tauraruwarta ba. Kyakkyawa kuma doguwar jarumar, wadda ta banƙara tsakanin manya ake damawa da ita tun farkon shigowarta masana’antar kannywood. Matsayin da ta hau a cikin shirin Hindu – An African Extra Vagrant haƙiƙa abun yabawa ne, ta bakin Hausafilm.

Shirin da ta fito a tsakkiyar manyan jarumai irinsu Adam A. Zango da Jamila Umar Nagudu. Yanayin yadda ta taka rawa a tsakkiyarsu tamkar ba macce ba ya ƙayatar da makallata. A wasu lokutan ma sai mutum ya mance da cewa macce yake kallo, dan ta yi tsayiwar daka wajen tabbatar da ganin ta taka muhimmiyar rawa a matsayinta na Bokanya.

Haka zalika batun kasuwa nan ma babu magana, dan tun bayan nuna shirin a Gidan kallon dake bisa hanyar Zoo Road a Kano, makallata sunka nuna maitarsu a fili ta mararin kallon shirin. Har ila yau ta samu yabo daga wajen manyan masana shirin kwaikwayo irin su Prof Abdallah Uba Adamu, Ahmad Gidan Dabino.

Fati Washa a jajircewarta a kannywood ta samu karramawa da shaidar yabo da dama a matsayinta na jaruma mai kwazo a shirin kwaikwayon da ta taka rawa. Kuma ƙarawa da ƙarau, Allah cikin rahamarshi a shekarar 2016 ya bata ikon zuwa Umrah a Saudi Arabiya.

8 Comments
 1. basheer ahmad says

  Ku sanya sharhinku…

 2. officer laouan says

  Na yaba sosai

 3. Ishak Washa Mai Waka says

  Allah Kabar mu Da Masoyan Mu

 4. Auwalu Yahuza Abdullahi says

  Ku sanya sharhinku… Fatan alkari a gare Ku

 5. Ibrahim kabir giwa says

  Allah yakara basira da tsawon rai mai amfani

 6. ALIYU ILYASU SDM says

  Your Comment…Gaskiya fati washa ina sanki amma kinfi kyau duk da haka inasonki

 7. IBRAHIM SANI says

  Your Comment IBRAHIM SANI GANTSA GASKIYA INA KAUNARKI,MUSLIM BOY,JIGAWA ST…

 8. Najeeb Noble says

  Masha Allah, Allah kara Daukaka

Leave A Reply

Your email address will not be published.