Yoruba

 • Hotuna: Nadin Sarautar Alh Yakubu Gobir a Garin Daura

  A Jiya Talata aka yi Wankan Sarautar Alhaji Yakubu Gobir a Daura, Jahar Katsina wanda yan uwa da abokan arziki daga sassa dabam-dabam na Nijeriya sunka halarta. Alhaji Yakubu Gobir Matasin Dan Kasuwa ne, Maitaimakawa Gajiyayyu, kana kuma Dan takarar Gwamna a Jahar Kwara, karkashin Tutar jam’iyar APC. Shine ya sayo Motoci dari biyu (200) ya bada dan yakin neman Zaben Shugaba Buhari da Mataimaki Osinbajo.

  Maimartaba Sarkin Daura, Dr. Alhaji Umar Farouk ya nada mai Sarautar Wazirin Hausa ganin irin taimakon da yake a Jahar Kwara da sauran Jahohi a Arewacin Nijeriya. Sardaunan Gobir, Dr. Ibrahim Abdullahi Gobir tareda tawagarshi sun halarci wannan wankan sarauta a Garin Daura. Allah ya taya Waziri riko.

  Ga ragowar hotunan daga taron nadin sarautar:

 • Hirar Fatima Ganduje da wata Jarida: Yadda soyayya ta hadani da mijina

  Fatima Ganduje diyace ga Gwamnan jahar Kano mai ci yanzu wadda akayi bikin aurenta da mijinta, ɗa ga Gwamnan jahar Oyo Idris Ajimobi a kwanakki. Shekarun Fatima 24 da haihuwa, ta kammala karatunta na jami’a da digiri mafi kima(first class) a jami’ar kasar Amurka dake jahar Adamawa (Abti). A cikin hirarsu da wata jarida Fatima ta bayyana yadda soyayya ta hadata da mijinta har sunka kai ga aure.

  A wata tattaunawa da editan City People yayi da ita, Fatima ta amsa wasu daga cikin tambayoyin da ya mata kamar haka:

  Da alama kina jin dadin rayuwar aurenki? Fatima ta amsa da cewa Eh, Tabbas hakane tun bayan da muka yi aure na kasance cikin farin ciki a gidan mijina.

  Shin zaki iya gaya mana yanda kuka hadu?, ta amsa da cewa dogon labarine amma a takaice, mun hadune sanadiyar wani dan uwanmu, kuma muna haduwa muka shaku da juna.

  Zaki iya gayamana kalmar farko da ya fara gayamiki lokacin da kuka hadu?, ta amsa da cewa, ya cemin zan iya sanin ko ke wacece, sai na amsa da cewa Eh, me zai hana.

  Tsawon wane lokaci kuka dauka kuna soyayya?, shekara daya da kusan rabi.

  Shin zaki iya gayamana wane irin mutum ne mijinki?, ta amsa da cewa mijina mutumin kirkine yana kula dani kuma dukkan abinda nake nema a tattare da miji yana dashi.

  Shin yaya kike kina kwalliya ki fito da kyau haka, tsawon wane lokaci kike dauka kina kwalliya?, sai ta amsa da cewa bana wani dadewa mintuna talatin kawai sun isheni, saboda nasan abinda zansa ya min kyau.

  Shin yaya zaki bayyana ‘yan uwan mijinki?, tace, suna son dan uwansu sosai kuma nima suna nunamin soyayya babu wani nuna banbanci.

  Shin a matsayinki na bahaushiya yaya kikeji da kika auri bayerabe?, sai tace, Ni ba bahaushiya bace, ni bafulatanace.

  Idan da ace bahaushe kika aura kina tunanin zaki samu babbanbancin soyayya?, sai tace ai soyayya ba ruwata da yare.

  Kin iya yarabanci? , sai tace a’a nadai dan fara koyo(tayi wani yarabanci kadan) tace amma tana sa ran nan gaba zata iya sosai haddama abincin yarbawa duk tana so ta iya.

  Ya zaki bayyana uwar mijinki?, tace mutumnjyar kirkice tana mun abinda ya kamata, bama uwar mijin bace uwatace.
  Thenet.ng

 • Gwamnan Ekiti ya sha rawani a taron Gwamnonin Jam’iyar PDP a Jahar Gombe

  Wasu zafafan hotuna sun bayyana a yanar gizo inda Gwamnan jahar Ekiti, Ayodele Fayose ya sha sabon rawani sanda yake halartar taron gwamnonin jam’iyyar PDP a jahar Gombe, gwamnan ya sha farin rawani irin na masu sarauta a taron Gwamnonin jiya Lahadi. Fayose yayi ƙaurin suna a matsayin dan adawar Shugaban kasar Nijeriya mai ci, tun kamin ma ya hau bisa kujerar mulki.

  Amman dai wannan karon rawanin ya ɗaukeshi.

 • Wankan Angwayen Fatima Ganduje

  Dan Gidan Gwamnan Jahar Oyo kenan Idris Abiola Ajimobi a wani hoto wanda wani mai daukar hoto, Tolani ya haska, ango tsakkiyar abokanshi suna murnar ranar auren abokinsu da Fatima Ganduje diyar Gwamnan Jahar Kano mai ci. Muna tayasu murna da fatan Allah ya bada zaman lafiya da ɗiya na gari. Ameen.

  Hotunan angwaye:

 • Hotuna: Matan Gwamnonin Arewa sun yi shigar Yarabawa a matsayin Uwayen Amarya

  Matan Gwamnonin Arewacin Nijeriya sun yi ankon bikin auren diyan Gwamnoni a ƙayatattar shiga irinta Yarabawa wadda suke kiraya “Aso ebi”, sune uwayen Amarya a wannan biki. Shagulgulan auren na Bayarabe Ajimobi da Bakana Fatima Ganduje wanda akai a Jahar Kano ya samu halartar Jami’an Gwamnati, Yan kasuwa, abokai da aminan arziki, wanda cikinsu harda su Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Aliko Dangote da Aminu Dantata.

  Hotunan Bikin Auren Fatima Ganduje da Ajimobi:

Close

Adblock Detected

Please consider supporting us by disabling your ad blocker