Tarihin Mamman Barka

  • Jamhoriyar Nijar: Mawaki Mamman Barka ya kwanta dama

    Ana zaman Makokin Shahararren Mawakin Gargajiya Alhaji Malam Mamman Barka wanda yayi gwagwarmaya dan raya al’adun Kasar Nijar. Allah ya ma mawakin rasuwa a safiyar yau Laraba, bayan fama da rashin lafiya. Mawakin wanda yana cikin mawakan da Nijar take ji dasu, yayi wakoki da dama cikin Harshen Hausa da Faransanci.

    Malam Mamman Barka an haifeshi a Garin Tesker dake Damagaram a Jahar Zinder. Ya rasu yana dan shekaru 59 da haihuwa. Ya bar mata daya da diya goma (10), biyar maza, biyar mata. Allah ya jikanshi da rahama.

Close

Adblock Detected

Please consider supporting us by disabling your ad blocker