Sakkwato

 • Shin Gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal ta san da Sabon Birni

  Shekarun Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na wa’adin shekara hudu a kan mulki sun kusa karewa amman har yanzu Gwamnatin ta kasa kawo karshen matsalar wutar lantarki a Sabon Birni lamarin da a shekarun baya tayi ikirarin shawo kan matsalar wanda duk da gyaran da Gwamnatin tace tayi amman har yanzu ba’a fi samun wutar wata ukku ba tunda ya hau mulki.

  Hakan na nuna bai damu da yan Sabon Birni ba duk da irin dimbin kuri’un da sunka zuba mai a zaben 2015 inda ya samu nasarar zama Gwamnan Jahar Sakkwato sannan kuma gashi wani zabe yana karatowa amman har yanzu babu ayyuka 3 masu girma da zai nuna ma Gobirawan karamar hukumar Sabon Birni a matsayin godiya. Koko dai a wannan zabe mai zuwa baya da bukatar kuri’ar su.

 • Daga karshe- Jam’iyar PDP ta bada sunan Gwamna Tambuwal a matsayin dan takarar Gwamna.

  A jiya Assabar 17 ga watan Nuwamba Jam’iyar PDP reshen Jahar Sakkwato ta maye gurbin Munir Dan’iya da sunan Gwamna Aminu Waziri Tambuwal a matsayin wanda zai yi takarar Gwamna karkashin jam’iyar PDP. Tunda farko dai rahotanni sun nuna cewa Gwamna Tambuwal dama yana da niyyar dawowa takarar Gwamna har idan dai baiyi nasarar samun tikitin tsayawa takarar Shugabancin kasa ba a jam’iyar PDP.

  Kasancewar yasha kaye inda Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya samu nasara, yanzu kuma zai kara da tsohon mataimakinai wanda yayi murabus kwanan nan Alh. Ahmed Aliyu Sokoto wanda kuma yaki binshi lokacin da ya sauya sheka zuwa jam’iyar PDP.

 • Dalilan da sunka sa Mataimakin Gwamnan Jahar Sakkwato yayi Murabus

  Jiya Laraba 14 ga watan Nuwamba Maigirma Mataimakin Gwamnan Jahar Sakkwato Alh. Ahmad Aliyu Sokoto ya aika ma majalisar dokokin Jaha wata takarda dauke da bayanin yayi murabus daga matsayinshi na Mataimakin Gwamna. Wannan dai yazo ne ana gab da gangamin fara neman zabe.

  Ahmad Aliyu dai tuni yaki bin Gwamnan Jahar Hon Aminu Waziri Tambuwal bayan ya sauya sheka daga Jam’iya mai Mulki ta A.P.C ya koma Jam’iyar adawa ta P.D.P a kokarinshi na ganin ya samu tikitin tsayawa takarar Shugaban kasa a jam’iyar P.D.P lamarin da yaci tura inda yazo na biyu a zaben fidda gwanin da Atiku Abubakar ya samu damar samun tikitin tsayawa takara shi kuma yazo na biyu.

  Sakamakon hakan dai jam’iyar A.P.C ta kyautata ma Ahmad Aliyu ta tsaida shi takarar gwamna wanda ana sa ran zai kara da ubangidanshi a zabe mai zuwa muddin P.D.P ta sauya dan takarar gwamnanta kamar yadda ake zato wanda yanzu haka Munir Dan’iya ne keyin takarar kafin a sauya shi da gwamna mai ci wanda dama amininshi ne.

Close

Adblock Detected

Please consider supporting us by disabling your ad blocker