Ranar Aure

 • Jarumar Kannywood, Maryam Booth zata yi aure

  Tauraruwar yar wasa a Masana’antar Kannywood, Maryam Booth da Saurayin da zai aureta wani tauraron Mawakin Hausa wanda ya shahara, ance sun jima suna sheke soyayyarsu a boye kamar yadda munka samo, sun bayyana soyayyar tasu wadda zata kare da aure.

  Hotunan nasu sun bazu a kafofin sada zumunta Maryam Booth(Dijangala) wadda ta haskaka akwatunan kallonku tun tana yarinya karama da saurayinta mai suna Sadik Zazzabi. Sun yanke shawarar zama ango da amarya in mai kowa mai komi ya yarda. Allah yasa albarka Dijangala.

  Ga hotunan Maryam Booth masu kama da na kamin biki:


 • Ado Gwanja tareda Amaryarshi Munat, Ya yo kalamin Soyayya

  Yau kimanin wata guda da auren Mawakin Mata da sahibarshi Maimuna, aure irin na soyayya da shakuwa da juna. Tauraron Mawakin kuma Jarumin barkwanci a Masana’antar Kannywood, Ado Isa Gwanja ya hauda wannan hotunan a kundinshi na wata kafar sada zumunta, ya rubuta cewa

  Zama da masoyi akwai dadi.

  Ya cigaba da cewa, Allah ka barmu mu rayu kamar haka ameen summa ameen.
  Muna musu fatan alheri.

 • Hotuna: Yau Ahmad Lawan ke Bikin Murnar cika Shekara 10 da Aure

  Kwanakki mun kawo muku labarin wannan Tsohon Jarumin Kannywood ɗin inda muka bayyana muku cewa yana neman takarar Dan Majalissa a Jahar Katsina ƙarƙashin tutar Jam’iyar APC. Ahmad Lawan ya watsa wasu kayatattun hotuna tareda matarshi da diyanshi ukku inda suka sha kyau. Masoya tareda abokan aiki ganin sakon da ya isar sukai caa suna ta tayashi murna da kasancewa tare cikin soyayya har tsawon shekaru goma(10) da samun zuri’a ɗayyaba.

  Mu ma muna tayaka murna Jarumi.

 • Amaryar Sarkin Ife tana share fagen zama Sarauniyar Masarautar Ile-Ife

  Sarkin Ife, Oba Adeyeye Ognwusi ya yo sabuwar amarya kwanan nan, watanni sha-hudu(14) bayan rabuwa da Tsohuwar Matarshi Sarauniya Wuraola Zaynab Otiti-Obanor bayan barkewar zargi tsakanin zaman aurensu.

  Sabuwar Amaryar, Olori Moronke Naomi Silekunola, wadda zata maye gurbinta hotunanta sun watsu a yanar gizo, inda aka ganta tana gudanarda wasu Al’adun Yarabawa na zama Sarauniya a Masarautar ta Ile-Ife a Jahar Ondo. A wannan hoton ta sanya kaya farare tana tsallaka jini, daga wannan sai wasu Dattizai suka mata rakkiya ga angon nata Sarki Oba Adeyeye Ognwusi.

  Mutanen garin suna ta farin ciki da maraba da Amaryar Sarkinsu.

 • Taurarun Kannywood sun haskaka Walimar Auren Abokin aikinsu, Adamu Isah Gwanja da Munat

  Taurarin Masana’antar Shirin Kwaikwayo, Kannywood, sun kece reni a Walimar Auren Abokin Aikinsu, cewa da Mawakin mata Adamu Isah Gwanja da Masoyiyarshi Maimunatu Kabeer Hassan. Walimar auren Ado Gwanja wanda aka yi a Birnin Kano ya samu halartar dubban dubatan masoya da abokan aikinshi irinsu, Mawakin Hausa Hiphop Adam A. Zango, Tauraruwar Kannywood Rukayya Dawayya wadda aurenta ya mutu kwanan baya, sai Maryam Yahaya Yar ƙwalisa da sauransu da dama.

  GobirMob na musu fatan Allah
  yasa ayi lafiya a gama lafiya.

  Maryam Yahayya ƴar ƙwalisa.

 • Hotunan kamin Biki na Auren Mawaki Ado Gwanja

  Kwanakki mun kawo muku labarin Soyayyar Mawakin Kannywood mai wake Mata da Budurwarshi Maimunatu Kabeer Hassan, wadda saboda so da kauna tun kamin auren nasu take ta haɗa sunanta da na angon nata a kafofin sada zumunta. Ɗamun auren Adamu Isa Gwanja da amaryarshi Munat zai gudana ran Assabar, 13 ga watan Oktoba 2018, kamar yadda ya bayyana a katin gayyata.

  Ga ƙayatattun hotunan auren Mawaki Ado Gwa na kamin aure:

 • Nafisa Abdullahi da Rahma Sadau tare wurin auren Ramadan Booth

  Masoyan taurarun Kannywood Rahma Sadau da Nafisa Abdullahi sun yi matukar farin cikin ganin yan wasan da basu ga maciji tare kasancewar sun sha sukar junansu a baya. Sun haska wasu kayatattun hotuna wanda sunka yi wurin shagalin bikin abokin aikinsu, Ramadan Booth da Fatima Ibrahim wanda aka yi ranar Assabar data gabata.

  Sun halarci bikin auren Ramadan Booth, wan abokiyar aikinsu Maryam Booth.

 • Tauraron dan wasan Kannywood, Ramadan Booth zai Angwance

  Ramadan Booth dazu-dazu ya watsa kayatattun hotunansu na kafin aure da sunka dauki hankula tareda masoyiyarshi- amaryar gobe a kundinshi na wata kafar sada zumunta. Dan wasan Masana’antar Kannywood din zai angwance da masoyiyar tashi ran Assabar 30 ga wata in Allah yaso.

  Ango Ramadan Booth da ne ga Zainab Booth, tsohuwar yar shirin kwaikwayo a Kannywood, Wa ga Maryam Booth(Dijangala) da Amude Booth wanda yayin Film din “Rashin Uwa.” A takaice dai yan gidansu Ramadan tun ba yau ba suke nishadankarda mu. Allah yasa ayi wannan aure lafiya a gama lafiya. Allah ya bada zaman lafiya da hankuri da juna. Ameen.

 • Tauraruwar Kannywood, Fati Washa ta bayyana irin Namijin da zata aura

  Fati Washa kyakkyawar jarumar Kannywood mai tashe dazu-dazun ga ta hauda wani sako a kundinta na wata kafar sada zumunta inda tayi rubutu danganeda irin namijin da take so ya zamo mijin da zata aura. Yana daga cikin nuna kula, masoya su rinka tambayar jarumai mata tambayoyi irinsu, “Yaushe zaki yi aure?”, “Aure shine martabarki”, “Mutumcin diya macce aure” da dai sauransu.

  A sakon nata ta rubuta cewa, “Ina son mu zama tareda wanda yakeda kulawa, wanda zai iya gane matsalolina, wanda  zai saurari kokena kuma wanda zai rinka sa ni dariya da farin ciki.”

  Ga hoton rubutun da tayi a harshen Ingilishi tacce:

 • Tauraron Kannywood Ibrahim Sharukan da amaryarshi sun yi shigar Indiyawa ranar aurensu

  Hoton sarkin masana’antar Kannywood kenan Ali Nuhu, tareda Jarumi Ibrahim Sharukhan da shi da amaryarshi sun yi shiga irinta Indiyawa ranar aurensu. Ibrahim jarumine da yafi fitowa a matsayin MC a hausa films, lakabin sunan sharukhan ya sameshi ne saboda son da yake ma wani jarumin Bollywood mai suna Sharukhan.

  Ali Nuhu, Ango da Amarya shiga ta yi kyau. Allah ya bada zaman lafiya. Ameen.

Close

Adblock Detected

Please consider supporting us by disabling your ad blocker