Niger

 • Shin ya dace Sarakunan Gargajiya su rinka taya ‘Yan Siyasa Yakin neman zabe?

  Wai tambaya muke wai ko ya dace Sarakunan mu na Gargajiya su rinka taya yan siyasar zamani yakin nenan zabe, ganin yadda abubuwa suke ta jujjuyawa suna ta sakewa- dan kar wata ran a wayi gari reshe ya juje da mujiya. Lalle Malam Bahaushe a wannan zamani ba zai iya gujewa barin al’adarshi ta gado ba illa abu guda da har yanzu ake martabawa wato Sarautar Gargajiya amman kash! sai gashi wasu daga cikin Sarakuna suna shirin susutarda wannan kima tasu inda suke nuna goyon bayansu ga wasu kwarorin yan siyasa duk da cewa sun kasance uwaye ne su ga kowa da kowa. Wanda hakan ya kawo cikas kwarai inda yan siyasa da zarar sun hau kujerr mulki sukan fara shirin korar duk wani mai sarauta da bai goyi bayansu ba su kuma nada duk wanda suke so walau ya cancanta da sarauta ko kuma bai cancanta ba musamman koda wasu sun kasance tsatson diya mata indai jinin sarauta ne to su babu ruwansu.

  Bugu da kari kuma mutanen gari a dalilin haka sukan fara ma sarauta rikon sakainar kashi inda da yawa daga cikin sarakuna yanzu basuda kima a wurin jama’ar da suke jagoranta wanda har idan ba’a shawo kan irin wannan matsala ba to nan gaba sai kaga an rinka ma sarakuna ihu, Allah dai yasa su rike martabarsu su bar kwadan abun yan siyasa.

 • Sanarwar taron Gobirawan Duniya wanda Jami’ar Usmanu Danfodiyo zata kaddamar dan karawa juna sani

  Muna farin cikin sanarda ku wani muhimmin taron kasa da kasa na farko(First International Conference) na Gobirawan duniya wanda Sashen Nazarin Larabci da Addinin Musulumci(Faculty of Arts and Islamic studies)Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sokoto zata kaddamar dan kara ma juna sani, daga ranar 9 ga watan Yuli zuwa 13. A baya wani sashen jami’ar ya gudanarda makamacin taron na Kabilar Kabawa, daya daga alummar Hausawa dake kewayeda Jahar ta Sakkwato. Za’a yi wannan taron a dakin taro na Jami’ar Usmanu Danfodiyo, University Auditorium.

  Shehunnan Masana Tarihi daga Jami’o’i wajen goma-sha-biyu (12) zasu halarci taron na kwanakki ukku dan gabatarda Tarihin da ya shafi Daular Gobir da Gobirawa; Asalin Gobirawa, Sarakunan da Gobir tayi, Asalin yaren Gobir, Alakar Gobirawa da sauran kabilu makwabta d.s.s wanda aka ma take “Masarautar Gobir, Jiya da Yau: Sauyi da Sauye-sauye- Gobir Kingdom, Past and Present: Transformations and Change.” Masana tarihin zasu zo daga Jami’o’i a Kasashen Afrika, Asiya, Turai da Kasashen Larabawa.

  Ga Sunayen Wasu Manyan Baki da Sarakan da zasu halarci taron:

  SHUGABAN TARO:
  Sanata Dr. Ibrahim Abdullahi Gobir
  Sanata Mai Wakiltar Yankin Sakkwato ta Gabas

  UWAYEN BIKI:
  Maimartaba, Sultan na Tsibiri,
  Alhaji Abdou Bala Marafa
  Jamhoriyar Nijar

  Mai martaba, Sultan na Sokoto
  Dr. Muhammad Sa’ad Abubakar

  KASIDU:
  Prof. Addo Muhamman
  Shugaban Jami’ar Tahoua
  Jamhoriyar Nijar

  Prof. Ila Maikasuwa
  Tsohon Ministan Ilimi Jamhoriyar Nijar

  Prof. Aliyu Muh’d Bunza
  Shugaban Sashen Ilimiya da Kimiyyar Danadam a Jami’ar Gusau

  MANYAN BAKI NA MUSAMMAN:
  Mai girma Rt Hon. Aminu Waziru Tambuwal (Matawallen Sakkwato)
  Gwamnan Jahar Sokoto

  Mai girma, Abdulaziz Abubakar Yari (Shettiman Marafa, Matawallen Zamfara) Gwamnan Jahar Zamfara

  Mai girma Sanata Atiku Bagudu (Matawallen Gwandu) Gwamnan Jahar Kebbi

  JIGOGIN JAWABI NA MUSAMMAN:
  Prof. Djibbo Mamman
  Shugaban Jami’ar Abdou moumini Niamey, Jamhoriyar Nijar

  Prof. Hakeem O Danmole
  Jami’ar Al-Hikmah Ilorin, Kwara Nigeria

  BABBAN MAI MASAUKIN BAKI:
  Prof. A.A Zuru
  Shugaban Jami’ar Usman Danfodio Sokoto

 • Masarautar Maradi ta kayyade kudin sadakin aure

  Masarautar Katsinar Maradi ta jamhoriyar Nijar dake karkashin ikon Sultan Ali Zaki ta bi sahun takwarorinta na Azbin da Damagaram wajen dakatarda yawan kashe kudi lokacin bukukuwan aure. Masarautar ta ce kudin sadaki da yake a jikka 33, kwatamcin dalar Amuruka 60 ya danganta da halin da mutum yake dashi idan zai kara saman wannan ya shefe shi, idan bai da hali kuma babu tilastawa.

  An dauki wannan kudurin ne bayan wani bincike da wata kungiya mai suna “Madallah” ta gudanar na yadda bukukuwa ke son gagarar mai karamin hali a ‘yan shekarun baya bayan nan.

  Binciken ya gano cewa irin wadannan sukan tilastama wasu zuwa su ciyo bashi domin suyi abunda yafi karfinsu.

 • Wani Dan Jamhoriyar Nijar yazo na ukku a Gasar karatun Alkur’ani ta duniya

  Hoton Idrissa Usman wani matashi daga kasar Nijar da yazo matsayi na ukku a musabakar karatun Al-Qur’ani Mai girma da ya gudana a kasar Kuwait wanda akai daga ran 12 zuwa 18 ga watan Afrilun 2018. Ya doke ƴan takara su wajen saba’in da tara.

  A gasar Nijar ta zo ta 3, bayan kasashen Libiya da Saudiyya cikin ‘yan takara 79.

 • Gwamnatin tarayya zata gina Matatar mai a Jahar Katsina tsakanin Iyakar Nijar da Nijeriya

  A jiya ne, karamin Ministan albarkatun Mai, Emmanuel I. Kachukwu ya kai ziyara jamhoriyar Nijar inda ya gana da Shugaban kasar, Muhammadou Issuhou aka kuma yi alkawarin gina Mamatar Mai a wani gari dake cikin Jahar Katsina tsakanin iyakar Nijar da Nijeriya.

  Haka kuma za’a ajiye bututu da zai rinƙa kawo ma Matatar Mai man da zata rinƙa tacewa daga Jamhoriyar Nijar ɗin. Nan gaba kaɗan za’a sanya ma takardun alkawarin hannu.

  Dalilin gina bututun mai da kuma hanyar jirgin kasa daga Nijeriya zuwa Nijar da Shugaban kasa, Muhammadu Buhari yayi alkawarin yi a jawabinshi na sabuwar shekara, ya fara fitowa fili, muna fatan Allah ya kara taimakon shuwagabannin mu akan ayyukan Alheri da suke yi.

 • President Buhari in Tahoua to attend Niger Republic 59 annivasary

  Nigerian President, President Muhammadu Buhari is in Niger Republic to attend 59th annivasary of proclamation of Niger a republic from French colonial masters. The annivasary hold on every 18 December in Niger states accordingly. In this year 2017, the annivasary will take place in Tahoua state, which before this date various renovation have been carried-out in cities and towns which they tagged (Tahoua sakola) cleansing Tahoua.

  The President will participate alongside Presidents of Mali, Burkina Faso, Chad, Mauritania and Niger.

  He is in company of Governor of Katsina Aminu Masari, Governor of Tobe Ibrahim Gaidam and Governor of Maiduguri Kashim Shettima.

Close

Adblock Detected

Please consider supporting us by disabling your ad blocker