Nadin sarauta

 • Hotuna: Nadin Sarautar Alh Yakubu Gobir a Garin Daura

  A Jiya Talata aka yi Wankan Sarautar Alhaji Yakubu Gobir a Daura, Jahar Katsina wanda yan uwa da abokan arziki daga sassa dabam-dabam na Nijeriya sunka halarta. Alhaji Yakubu Gobir Matasin Dan Kasuwa ne, Maitaimakawa Gajiyayyu, kana kuma Dan takarar Gwamna a Jahar Kwara, karkashin Tutar jam’iyar APC. Shine ya sayo Motoci dari biyu (200) ya bada dan yakin neman Zaben Shugaba Buhari da Mataimaki Osinbajo.

  Maimartaba Sarkin Daura, Dr. Alhaji Umar Farouk ya nada mai Sarautar Wazirin Hausa ganin irin taimakon da yake a Jahar Kwara da sauran Jahohi a Arewacin Nijeriya. Sardaunan Gobir, Dr. Ibrahim Abdullahi Gobir tareda tawagarshi sun halarci wannan wankan sarauta a Garin Daura. Allah ya taya Waziri riko.

  Ga ragowar hotunan daga taron nadin sarautar:

 • Hotuna: Nadin sarautar shahararren Dankasuwar Maradi a Tsibirin Gobir

  A ranar lahadine daidai da 24 ga watan Dicemba 2017 aka yi wankan sarautar Elhj Sani Bala Dansani a Tibiri Gobir. Sani Bala shahararren dankasuwa ne kuma dansiyasa a Jahar Maradi, Jamhoriyar Nijar. Sani Bala ɗa ne ga margyayin dan kasuwa a jahar, cewa da Elhj Bala Dansani, Allah ya jikanshi da rahama.

  An naɗa Sani Bala Dan garan Gobir wadda da alamu sarautace tasu ta gado. Manyan bakin da sunka hallara a taron sun haɗa da sarakan Gobir daga Nijar da Nijeriya, Jami’an Gwamnati, Yan Siyasa da Yan Kasuwa, gamida yanuwa da abokan arziki. Bayan shi an yi sauran nade-naden sarautar mutane biyar da sunka haɗa da Injiniyan noma, Engr. Jika Naino wanda aka naɗa Dangaladiman Gobir, Dankasuwar Dakoro Malam Ousmane Balla Na-Allah da aka naɗa Masarin Gobir, Dankasuwa a Boungugi Elhj Chaibou Oumarou da aka nada Barden Gobir, Mashari’anci(Advocate) a Birnin Yamai Malam Laouali Amadou Madougou shi kuma aka nadashi kadon Gobir, sai kuma Dankasuwa a Birnin Tsibiri Malam Abou Gonda da aka naɗa sarautar Dangaladiman Sarkin Fawan Gobir.

  Sarautar Dan gara a Gobir, ta bakin Sani Danbieto Gobir, ma’anarta shine Sarki baya bada umarnin yaki sai da sa bakin Dan gara. A takaice sarautar dangara sauratace ta shawara kan harkokin da sunka shafi yaki a da.

Close

Adblock Detected

Please consider supporting us by disabling your ad blocker