Labaran Gobir

 • Shin Gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal ta san da Sabon Birni

  Shekarun Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na wa’adin shekara hudu a kan mulki sun kusa karewa amman har yanzu Gwamnatin ta kasa kawo karshen matsalar wutar lantarki a Sabon Birni lamarin da a shekarun baya tayi ikirarin shawo kan matsalar wanda duk da gyaran da Gwamnatin tace tayi amman har yanzu ba’a fi samun wutar wata ukku ba tunda ya hau mulki.

  Hakan na nuna bai damu da yan Sabon Birni ba duk da irin dimbin kuri’un da sunka zuba mai a zaben 2015 inda ya samu nasarar zama Gwamnan Jahar Sakkwato sannan kuma gashi wani zabe yana karatowa amman har yanzu babu ayyuka 3 masu girma da zai nuna ma Gobirawan karamar hukumar Sabon Birni a matsayin godiya. Koko dai a wannan zabe mai zuwa baya da bukatar kuri’ar su.

 • Hon Yusuf Muhammad Gobir- Shugabannin APC na Sabon Birni tsintsiya ne madauri daya

  Maigirma dan Majalisar Jaha Mai wakiltar Sabon Birni ta Arewa Hon Yusuf Muhammad Gobir wanda yana daya daga cikin ‘yan majalissu 12 da suka tsaya a jam’iyar APC bayan sauya shekar Gwamna Tambuwal zuwa PDP, A ranar Assabar da ta wuce ya kara jaddada ma magoya bayan APC na karamar hukumar mulkin cewa su fa shugabannin da kuma masu hannu da shuni na jam’iyar A.P.C na karamar hukumar Sabon Birni suna nan dunkule sun zama tsintsiya madaurinki daya.

  Hon Yusuf dai ya fadi hakan ne a lokacin da magoya bayan jam’iyar A.P.C sunka kawo mai ziyara a gidanshi dake shiyar tudun wada Sabon Birni inda yake shaida musu cewa duk wani dake kishi da kuma son cigaban wannan karamar hukuma ta Sabon Birni to yana nan daram a APC dan su cigaban al’umma shine sunka sa gaba.
  Hon Yusuf dai ya kara kira ga jama’a da su guji duk wani abu da zai kawo fitina inda yake musu nuni da cewa babban makamin talaka shine kuri’a dan haka babu bukatar wani tada da hankali illa dai suyi ta addu’a Allah yasa a kare wannan zabe lami lafiya.

Close

Adblock Detected

Please consider supporting us by disabling your ad blocker