Katsina

 • Daga littafin My Transition hours: Babban dalilin da yassa na ba Buhari Mulki a 2015

  Maigirma Tsohon Shugaban kasar Nijeriya Dr. Goodluck Ebele Jonathan karshe ya bayyana daya daga cikin dalilan da yassa ya aminta da sakamakon zaben 2015 a littafin da ya kaddamar kwanakki, inda yake bayyana cewa tsoron halin da ‘yan Kudu Mazauna Arewa ne zasu shiga shi yassa ya yarda da cewa an kada shi.

  Jonathan dai ya bayyana hakan ne ta wani littafin shi daya kaddamar a kwanannan wanda ya ma lakabi da sun “MY TRANSITION HOURS” inda yake bayyana cewa muddin bai yarda ba to hakan na iya jawo a yima ‘yan kudu mazamna Arewa kisan kiyashi.

  Tunda farko dai masana sunyi hasashen cewa muddin aka kada Jonathan to yana da wahala ya yarda ya mika mulki cikin ruwan sanyi amman sai gashi cikin wani alamari mai cike da mamaki da kuma tarihi a siyasar Nijeriya Tsohon Shugaba Jonathan ya kira Shugaba Buhari ya tayashi murnar lashe zabe tare da daukar kaddarar cewa ya fadi tunma kafin hukumar zabe ta bayyana cikakken sakamako lamarin da yassa har yanzu Shugaba Buhari yake ganin mutumcin Jonathan na irin kawar da fitinar da yayi.

 • Hotuna: Nadin Sarautar Alh Yakubu Gobir a Garin Daura

  A Jiya Talata aka yi Wankan Sarautar Alhaji Yakubu Gobir a Daura, Jahar Katsina wanda yan uwa da abokan arziki daga sassa dabam-dabam na Nijeriya sunka halarta. Alhaji Yakubu Gobir Matasin Dan Kasuwa ne, Maitaimakawa Gajiyayyu, kana kuma Dan takarar Gwamna a Jahar Kwara, karkashin Tutar jam’iyar APC. Shine ya sayo Motoci dari biyu (200) ya bada dan yakin neman Zaben Shugaba Buhari da Mataimaki Osinbajo.

  Maimartaba Sarkin Daura, Dr. Alhaji Umar Farouk ya nada mai Sarautar Wazirin Hausa ganin irin taimakon da yake a Jahar Kwara da sauran Jahohi a Arewacin Nijeriya. Sardaunan Gobir, Dr. Ibrahim Abdullahi Gobir tareda tawagarshi sun halarci wannan wankan sarauta a Garin Daura. Allah ya taya Waziri riko.

  Ga ragowar hotunan daga taron nadin sarautar:

 • Zaben 2019: Ra’ayoyin Taurarun Kannywood, Kwararru, Yadda zasu kai Yan Takara ga ci

  Tun bayan da taurarun yan wasan kwaikwayo sun ka kasu gida biyu, magoya bayansu ke ta tunanin yadda wannan kasuwar tasu zata sa yan takarar da suke goyon baya su kai ga nasara. Ganin yadda a baya 2015 sun hada kawuna dan kai Buhari ga ci da salo irin nasu na nishadi da wayarda kan masu zabe, ya kada Tsoho Shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan.

  Bayanai sun nuna cewa ba’a taba samun adadin jaruman Kannywood da sunka fito fili sun ka nuna alkiblarsu ba kamar a wannan lokacin. Hasalima, tuni manyan jarumai irinsu Ali Nuhu da Adam A. Zango da Fati Washa sunka ziyarci fadar shugaban kasa dake Abuja inda sunka bayyana shirinsu na marawa Shugaba Muhammadu Buhari baya a yunkurin da yake na sake lashe zaben 2019.

  Hakazalika, Jarumai irinsu Sani Danja, Fati Muhammad, Maryam Booth, Mika’ilu Bn Hassan Gidigo sun sha alwashin ganin Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa a shekarar 1999-2007, Alhaji Atiku
  Abubakar, wanda ke takarar shugabancin Nijeriya a inuwar Jam’iyyar PDP, ganin ya samu nasara a zaben 2019.

  A tattaunawar da BBCHausa tayi da fitaccen mai ruwa da tsaki a Kannywood kuma Shugaban hukumar tace faifaye ta Jahar Kano, Isma’ila Naabba Afakallah, yace jaruman Kannywood suna da muhummiyar rawar da zasu taka wajen ganin an samu Shugabanci na gari a kasar. Afakallah, wanda ke goyon bayan Shugaba Buhari, ya kara da cewa “Muna da miliyoyin magoya baya wadanda ko ka so ko ka ki zasu yi abunda muke so suyi saboda kaunar da suke ma masana’antar Kannywood: ciki kuma harda zaben mutunen da muke son su zaba.”

  Ga tashi cewar, tsunduma cikin harkokin siyasa da taurarun sunka yi wata alama ce dake nuna cewa sun bar nade hannuwansu wurin sha’anin shugabanci ko da ba za a basu ko taro ba.

  A bangaren fitaccen jarumi kuma furodusa, Falalu Dorayi, ya bayyana min cewa sabanin takwarorinsu na Amurka – wadanda yan takarasu suka sha kaye a zaben Amurka – ‘yan wasan kwaikwayon Hausa suna da magoya bayan da ba zasu kwance musu zane a kasuwa. “Idan ka yi waiwaye za ka ga cewa a zaben 2015 mun yi kira ga magoya bayanmu su fito kwansu da kwarkwatarsu su zabi Muhammadu Buhari, kuma hakan aka yi. “Dan haka ina ganin yanzu ma za a kwata. Bani shakkar amincin da ke tsakaninmu da magoya bayanmu,” in ji shi. Wanda zai cika alkawari kawai zamu sa su zaba’

  Sai dai Mika’ilu Gidigo ya ce duk da yake taurarin yan wasan Kannywood
  na iya sauya alakar masu zabe amma masu kada kuri’a zasu zabi mutumen da suke ganin yana da cika alkawari ne kawai. “Ina so ka san cewa mutane dabam suke. Mu a Nijeriya duk da goyon bayan da masu kallo suke yi muna ba za su zabi wanda bai cika musu alkawari ba. “Idan ka dubi baya za ka ga cewa Shugaba Buhari ya yi alkawuran kawo sauye-sauye amman a zahiri adadin matasan da ba su da aikin yi yanzu ya fi na baya; mutanen da ke
  kwana da yunwa yanzu sun zarta na baya. “Dan haka zamu ba masu kallonmu hujjoji ingantattu wadanda zasu hana su sake zaben Shugaba Buhari a 2019,” In ji Gidigo.

  A yayin da jarumai irin su Adam Zango, ke cewa suna goyon bayan Shugaba Buhari ne ba dan ya samu ko sis ba, sai dan dai kawai ya gamsu da salon shugabancin nashi ne, sannan Fati Muhammad, ke jaddada kiraye-kirayen da take yi cewa tana goyon bayan Alhaji Atiku Abubakar ne saboda gwamnatin Buhari ta gaza kawo sauyin da ta yi alkawarin yi ga ‘yan kasar – masu sharhi sun yi ma batun kallon tsanaki. Ra’ayin masu sharhi Mallam Muhsin Ibrahim, wani masani kan harkokin Kannywood wanda kuma ke koyarda Ilmin wasan kwaikwayo a Jami’ar Birnin Colonge na kasar Jamus, ya ce akwai yiwuwar jaruman Kannywood su yi tasiri kan masu kallonsu wajen zaben shugabanni saboda yanayin wayewa da sanin ‘yancin kai da ilimin Amurkawa daban yake da na ‘yan Najeriya. “Eh, ina ganin jaruman yan wasan kwaikwayo zasu iya sauya tunanin masu kallonsu dan su zabi dan takarar da suke kauna. “Kar ka manta matakin tunani da ilimin masu zabe a Amurka dabam yake da na ‘yan Nijeriya. Yawancin masu kallon yan wasan Kannywood suna yi musu soyayya tamkar bauta don
  haka za su iya yin duk abunda suka sa su.” Sai dai Dr. Daha Tijjani, wani Malami a jami’ar Limkokwing da ke Malaysia, wanda ya rubuta kundin digirin
  digirgir din shi a kan tasirin da ‘yan
  wasan kwaikwayo suke yi wajen sauya tunanin al’umma, ya ce masu kallon faifayen bidiyon masana’antar Kannywood, musamman matasa sun fi yarda da abunda ake kira “Sayen-na-gari mai-da-kudi-gida” ba wai abunda wani dan wasa ya ce suyi ba. Ga tashi cewar, ko da ‘yan wasan kwaikwayo sun bukaci masu kallonsu su zabi mutum ba zasu yi hakan ba sai idan suna ganin zai iya kawo sauyi a rayuwarsu. Gani ga wane Ganin yadda ‘yan fim a Najeriya suka shiga harkokin siyasa ta hanyar nuna goyon baya kara ga ‘yan takara, ga alama za a zuba ido dan
  ganin ko Taurarun yan wasan Kannywood zasu iya sauya akalar zaben 2019, musamman idan aka yi la’akari da cewa takwarorinsu na Amurka, sun ji kumya, sakamakon yadda ‘yan takarar da suka mara ma baya suka gaza kai labari.

  Alkaluman zaben tsakkiyar wa’adin mulki da aka gudanar a Amurka a makon jiya sun suna cewa taurarun yan wasa da mawaka ba su iya yin tasiri wurin ganin ‘yan takara sun ci zabe. Bayanai da dama sun nuna yadda duk da miliyoyin mabiyan da
  wadannan taurari ke da su, basu iya taimakawa ‘yan takarar da suka mara wa baya wurin cin zabe. Misali, har zuwa ranar zabe, Beyonce ta fito fili ta goyi bayan dan jam’iyyar Democrat Beto O’Rourke a zaben majalisar dattawan Jahar Texas – sai dai Sanata mai-ci Ted Cruz ya kada da shi. Hakazalika, Rihanna ta yi kira ga magoya bayanta a Florida su zabi Andrew Gillum

 • Hotuna: Yau Ahmad Lawan ke Bikin Murnar cika Shekara 10 da Aure

  Kwanakki mun kawo muku labarin wannan Tsohon Jarumin Kannywood ɗin inda muka bayyana muku cewa yana neman takarar Dan Majalissa a Jahar Katsina ƙarƙashin tutar Jam’iyar APC. Ahmad Lawan ya watsa wasu kayatattun hotuna tareda matarshi da diyanshi ukku inda suka sha kyau. Masoya tareda abokan aiki ganin sakon da ya isar sukai caa suna ta tayashi murna da kasancewa tare cikin soyayya har tsawon shekaru goma(10) da samun zuri’a ɗayyaba.

  Mu ma muna tayaka murna Jarumi.

 • Sanarwar taron Gobirawan Duniya wanda Jami’ar Usmanu Danfodiyo zata kaddamar dan karawa juna sani

  Muna farin cikin sanarda ku wani muhimmin taron kasa da kasa na farko(First International Conference) na Gobirawan duniya wanda Sashen Nazarin Larabci da Addinin Musulumci(Faculty of Arts and Islamic studies)Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sokoto zata kaddamar dan kara ma juna sani, daga ranar 9 ga watan Yuli zuwa 13. A baya wani sashen jami’ar ya gudanarda makamacin taron na Kabilar Kabawa, daya daga alummar Hausawa dake kewayeda Jahar ta Sakkwato. Za’a yi wannan taron a dakin taro na Jami’ar Usmanu Danfodiyo, University Auditorium.

  Shehunnan Masana Tarihi daga Jami’o’i wajen goma-sha-biyu (12) zasu halarci taron na kwanakki ukku dan gabatarda Tarihin da ya shafi Daular Gobir da Gobirawa; Asalin Gobirawa, Sarakunan da Gobir tayi, Asalin yaren Gobir, Alakar Gobirawa da sauran kabilu makwabta d.s.s wanda aka ma take “Masarautar Gobir, Jiya da Yau: Sauyi da Sauye-sauye- Gobir Kingdom, Past and Present: Transformations and Change.” Masana tarihin zasu zo daga Jami’o’i a Kasashen Afrika, Asiya, Turai da Kasashen Larabawa.

  Ga Sunayen Wasu Manyan Baki da Sarakan da zasu halarci taron:

  SHUGABAN TARO:
  Sanata Dr. Ibrahim Abdullahi Gobir
  Sanata Mai Wakiltar Yankin Sakkwato ta Gabas

  UWAYEN BIKI:
  Maimartaba, Sultan na Tsibiri,
  Alhaji Abdou Bala Marafa
  Jamhoriyar Nijar

  Mai martaba, Sultan na Sokoto
  Dr. Muhammad Sa’ad Abubakar

  KASIDU:
  Prof. Addo Muhamman
  Shugaban Jami’ar Tahoua
  Jamhoriyar Nijar

  Prof. Ila Maikasuwa
  Tsohon Ministan Ilimi Jamhoriyar Nijar

  Prof. Aliyu Muh’d Bunza
  Shugaban Sashen Ilimiya da Kimiyyar Danadam a Jami’ar Gusau

  MANYAN BAKI NA MUSAMMAN:
  Mai girma Rt Hon. Aminu Waziru Tambuwal (Matawallen Sakkwato)
  Gwamnan Jahar Sokoto

  Mai girma, Abdulaziz Abubakar Yari (Shettiman Marafa, Matawallen Zamfara) Gwamnan Jahar Zamfara

  Mai girma Sanata Atiku Bagudu (Matawallen Gwandu) Gwamnan Jahar Kebbi

  JIGOGIN JAWABI NA MUSAMMAN:
  Prof. Djibbo Mamman
  Shugaban Jami’ar Abdou moumini Niamey, Jamhoriyar Nijar

  Prof. Hakeem O Danmole
  Jami’ar Al-Hikmah Ilorin, Kwara Nigeria

  BABBAN MAI MASAUKIN BAKI:
  Prof. A.A Zuru
  Shugaban Jami’ar Usman Danfodio Sokoto

 • Masarautar Maradi ta kayyade kudin sadakin aure

  Masarautar Katsinar Maradi ta jamhoriyar Nijar dake karkashin ikon Sultan Ali Zaki ta bi sahun takwarorinta na Azbin da Damagaram wajen dakatarda yawan kashe kudi lokacin bukukuwan aure. Masarautar ta ce kudin sadaki da yake a jikka 33, kwatamcin dalar Amuruka 60 ya danganta da halin da mutum yake dashi idan zai kara saman wannan ya shefe shi, idan bai da hali kuma babu tilastawa.

  An dauki wannan kudurin ne bayan wani bincike da wata kungiya mai suna “Madallah” ta gudanar na yadda bukukuwa ke son gagarar mai karamin hali a ‘yan shekarun baya bayan nan.

  Binciken ya gano cewa irin wadannan sukan tilastama wasu zuwa su ciyo bashi domin suyi abunda yafi karfinsu.

 • Wani Dan Jahar Katsina ya kirkiro maganin makanta da duniya ta yaba dashi

  Dakta Bashir Dodo wani hazikin likita wanda ya fito daga Jahar Katsina yayi abun yabo da duniya ta jinjina mishi. Gasar wadda akayi wannan shekara 2018 a kasar Portugal, Bashir yazo da wani tsari wanda zai taimaka cikin gaggawa wajen magance ciwon makanta, hakan yasa Bashir ya zamo na daya a tsakanin dalibai da suka fafata a wannan gasar.

  Bahaushen ya sake lashe wata gasar daukar hotunan sassan jikin mutane wadda akeyi dan kawo cigaba a harkar kula da lafiyar ‘yan Adam.

  Bashir yayi karatun digirin koli na Dakta a wata jami’ar kasar Ingila.

  GobirMob na mishi fatan Alheri da kuma fatan Allah ya kara basira. Ameen.

 • Tarihin yakin Katsinawa da Gobirawa

  A zamanin Sarkin Gobir Muhammane Mai-Gicce, sarkinda yayi sarauta a Gwararrame a yankin Gidan Rumji(Guidan Roumdji) ta yanzu a Jahar Maradi, Jamhoriyar Nijar. A zamanin wannan sarki ya tanadi wani asiri wanda ake kira da “Gicce”, shi wannan asiri shine sanadiyar da yassa ake mai lakabi da Sarki Gobir Mai-Gicce. Amfanin wannan asirin ga masarautar shine gudun farmakin bazata da kariya daga abokan hamayya da duk rundunardar yakin da ta nuho masarautar da niyyar yaki. Ko da labari yazo ga fada cewa ga rundunar yaki nan tafe ko an tsinkayo ƙura daga nesa alamar gudanar dawakai sai ayi maza-maza a sanardar mai ɗauko asirin. Runduna na isowa gab da gari sai a ɗaga Gicce sama. Da zarar an ɗagashi sama sai ƙura ta turnuƙe su kuma abokan gaba sai su kama gabansu dan tsoron abunda zai biyo baya garesu inda su kuma mayaƙan Gobir sun shirya kayan yaƙinsu cib-cib.

  Sarkin Katsina Janhazo a lokacin Tsohuwar Masarautar Katsina ta wancan lokaci tana karɓo umarni daga Masarautar Gobir, Sarkin da ganin Gobir bata yaƙuwa su kuma dama sunsan dalili shine sai sunka yo shiryayya da dubara na yaƙar Uwar Masarautarsu. Kafin su zo ma Gobir da yaƙi saida sunka yo dubara sunka raba Masarautar Gobir da wannan Asirin. Daga baya sai Katsina ta taho da rundunarta ta neman suna ta kafa tarihi a matsayin ƙabilar hausa da ta taɓa yaƙar ƴar uwarta da sunan yaƙi. A wannan labarin, sabanin yadda su sunka sha bada tarihin, zaku ji yadda tabbataccen tarihin yakin ya wakana, yadda Katsinawa sunka yaudari Gobirawa, sunka yakesu.

  Tarihin yakin Katsinawa da Gobirawa, kamar yadda Sarkin Gobir na Tsibirin Gobir ya bada a Gidan Talabijan na Kasar Jamhoriyar Nijar, Tele Sahel.

  Sultan Abdourahamane Bala Marafa sanda yake bada amsar tambayoyin da Danjarida ke mai na Tarihin Daular Gobir a daure, Alakarsu da zaman da suka yi da kabilu makwabta irinsu Barebari da Zabarmawa a da can. Sarki ya kuma yi karin haske gameda Tarihin Zaman Danfodio a Birnin Alkalawa da Tarihin Yakin Danfodio da Yunfa, Gwagwarmaya tsakaninshi da Sarki Bawa Jangwarzo, Sarki Nafata da Sarki Yakubu. Danjaridar Bazabarme ya sake tambayar Mai Martaba Tarihin Yakin Gobirawa da Katsinawa.

  *Ku tarbemu a kashi na biyu dan samun wannan tarihi*

Close

Adblock Detected

Please consider supporting us by disabling your ad blocker