Jaruman Kannywood

 • Ziyarar Taurarun Kannywood Gidan Atiku Abubakar, cikin hotuna

  Taurarun Yan Wasan Shirin Kwaikwayo da Mawakan Hausa masu goyon bayan Dan Takarar Shugaban
  kasar Nijeriya na jam’iyyar PDP, Atiku
  Abubakar sun kai mai ziyara har gidainda
  sunka bayyanashi a matsayin dan
  takararsu.

  A jawabin da yayi lokacin ganawar tasu, Atiku
  ya bayyana cewa, yaji dadin ziyarar
  jaruman da sunka kaimai kuma ya yaba da kokarin da suke yi na ganin ya samu nasara a zabe mai zuwa. Cikin jaruman da sunka kai
  ziyarar akwai tauraru irinsu Abba El-Mustafa, Fati
  Muhammad, Abida Muhammad,
  Zaharaddeen Sani da dai sauransu.

 • Maryam Yahayya Jarumar Kannywood ta aikoda Gaisuwar Juma’a ga masoyanta

  Jarumar Kannywood sabuwar tashe, Maryam Yahaya, dazu da safe ta hauda wasu hotunan inda ta rambada kolliya ta manyan yanmatan. Maryam ta hauda hotunan a kundinta na wata kafar sada zumunta ta kara da aikoda gaisuwar barka da Juma’a ga masoyanta a dandalin.

  Ga rubuntun nata:

  Barkada juma’a

 • Soyayya: Jarumin Kannywood, Adam A Zango yana sumbuntar matarshi yar Kamaru

  Ummulkulsum kyakkyawar matar shahararren dan wasan Kannywood ce yar asalin kasar Kamaru wadda ya aura a shekarar 2015, itace cikon matan jarumin na ukku ko hudu duk da cewa ya taba sakin wasu a baya. Adam A. Zango ya watsa waɗannan hotunan ne tareda amaryar tashi suna sheƙe soyayya, harda sumbunta.

  Prince Zango ya watsa hotunan ne a kundinshi na kafar sada zumunta, Instagram, wanda masoya dake bibiyarshi suka ta yabawa tareda masu addu’ar zaman lafiya.

  Zango fitaccen jarumin Kannywood ne da ya sha karramawa da kyaututtuka daga kungiyoyin shirin kwaikwayo, saboda fitattun shirin da yake fitowa garesu da wanda yake shiryawa a masana’antar ta shirin kwaikwayo.

Close

Adblock Detected

Please consider supporting us by disabling your ad blocker