hausa

 • Hotuna: Jarumin Nollywood, Talle na murnar cika shekara 41 da haihuwa

  Shahararren Jarumin kudancin Nijeriya, Nollywood, Chinedu Ikedieze wanda kun ka fi sani da “Talle” yau yake murnar zagayowar ranar haihuwarshi inda ya haska wasu kayatattun hotuna na nuna farin ciki. Da shi da abokinai Osita Iheme ko kuce “Mudi” sun sha fitowa a faifayen shirin Nollywood inda sunka yi fice ba ma a Afrika ba kadai har saura kasashe Turai irin su Rasha, Crotia, Amerika dss kuma sun sha daukar kambunan yabo. Margyayi Rabilu Musa DanIbro ya taba musu hanyar fitowa a wani shiri Karangiya wanda sanadiyar haka sunka dada yin suna a duniyar masoyan Kannywood.

  An haifi Talle ran 12 ga watan Dicamba, 1977
  a shiyar Bende dake Jahar Abia Nijeriya.

 • Gatan-gatanku- Gatanar Kura Da Dan Tumkiya

  Wannan gatanar Kura ce da Dan Tumkiya. Gatanan, gatananku. Ta je ta dawo. Wata rana kura tana yawo sai ta hangi dan Tumkiya yana shan ruwa a gefen hanya sai nan-da-nan tayi tunanin dubarar da zata yi ta kasheshi, nan take sai ta gusa inda yake shan ruwa kamar itama zata sha sai tace ma shi, “Ta yaya zaka bata ruwan da nake sha” jikinshi na rawa yace ranki shi dade ta yaya zanyi haka ai ma kuma ruwan ta wurinki su ka fara biyowa sannan su iso gareni. Sai kura ta sake ce ma shi, “Aima shekarar data wuce kaine ka la’anci uwata” Sai yace aini shekarar data wuce bama a haifeni ni ba. Da taji haka sai tace to lalle zakayi ta ‘yan dubarunka amman yau sai na lakume ka. Kunkur kan kusu.
  DARASI
  Wannan yana nuna muna idan har mutum yayi niyyar kulla sharri a rayuwarshi to komi girman hujjoji da gaskiyar da za’a nuna ma shi ba zai hana shi aikatawa ba. Allah yasa mu kasance masu aikata alheri Amin.

 • Hotuna: Zinder ta shirya tsab dan tarben Bikin 18 Decembre 2018

  A Jamhoriyar Nijar, kowace shekara Gwamnatin kasa na ware makuddan kudade dan yin aikace-aikace da sunka haɗa da gine-ginen zamani da kwaskwarima birnin da kauye saboda babban bikin ranar da Nijar ta zama kasa mai cikakken yanci daga Turawan Mulkin Mallaka, Faransawa. Wannan shekarar, ranar 18 ga Disamba, Jahar Zinder zata baƙunci wannan biki inda tun bara 2017 ake ta kolliya mai taken “Zinder Sabouwa.” Saboda haka GobirMob ta kutsa ta kawo muku hotunan Sabuwar Zinder ɗin dan ku ba idanuwanku abunci.

  Masana tarihi sunce a Jahar Zinder aka farashi lokacin tana zaman Babban Birnin kasar kafin daga bisani aka tashi aka koma Niamey saboda matsalar ruwa da ta addabi garin Damagaram. An kuma ce Malamai da sunka ga irin bala’in da ake tabkawa a garin na Malamai, shi yassa Damagarawa sunka dage da addu’o’in ba dare ba rana har Allah ya kawo matsalar ruwa da ta sa aka bar garin.

  Anyi na Diffa 2013, Dosso Sogha 2014, Maradi Kolliya 2015, Tahoua Sakola 2016, Agadez Sokni 2017, bana 2108 za’a yi na Zinder, Zinder Sabouwa. Allah yasa a yi lafiya, a gama lafiya.

  Ga hotunan Zinder Sabouwa:


 • Shin ya dace Sarakunan Gargajiya su rinka taya ‘Yan Siyasa Yakin neman zabe?

  Wai tambaya muke wai ko ya dace Sarakunan mu na Gargajiya su rinka taya yan siyasar zamani yakin nenan zabe, ganin yadda abubuwa suke ta jujjuyawa suna ta sakewa- dan kar wata ran a wayi gari reshe ya juje da mujiya. Lalle Malam Bahaushe a wannan zamani ba zai iya gujewa barin al’adarshi ta gado ba illa abu guda da har yanzu ake martabawa wato Sarautar Gargajiya amman kash! sai gashi wasu daga cikin Sarakuna suna shirin susutarda wannan kima tasu inda suke nuna goyon bayansu ga wasu kwarorin yan siyasa duk da cewa sun kasance uwaye ne su ga kowa da kowa. Wanda hakan ya kawo cikas kwarai inda yan siyasa da zarar sun hau kujerr mulki sukan fara shirin korar duk wani mai sarauta da bai goyi bayansu ba su kuma nada duk wanda suke so walau ya cancanta da sarauta ko kuma bai cancanta ba musamman koda wasu sun kasance tsatson diya mata indai jinin sarauta ne to su babu ruwansu.

  Bugu da kari kuma mutanen gari a dalilin haka sukan fara ma sarauta rikon sakainar kashi inda da yawa daga cikin sarakuna yanzu basuda kima a wurin jama’ar da suke jagoranta wanda har idan ba’a shawo kan irin wannan matsala ba to nan gaba sai kaga an rinka ma sarakuna ihu, Allah dai yasa su rike martabarsu su bar kwadan abun yan siyasa.

 • Shin Gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal ta san da Sabon Birni

  Shekarun Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na wa’adin shekara hudu a kan mulki sun kusa karewa amman har yanzu Gwamnatin ta kasa kawo karshen matsalar wutar lantarki a Sabon Birni lamarin da a shekarun baya tayi ikirarin shawo kan matsalar wanda duk da gyaran da Gwamnatin tace tayi amman har yanzu ba’a fi samun wutar wata ukku ba tunda ya hau mulki.

  Hakan na nuna bai damu da yan Sabon Birni ba duk da irin dimbin kuri’un da sunka zuba mai a zaben 2015 inda ya samu nasarar zama Gwamnan Jahar Sakkwato sannan kuma gashi wani zabe yana karatowa amman har yanzu babu ayyuka 3 masu girma da zai nuna ma Gobirawan karamar hukumar Sabon Birni a matsayin godiya. Koko dai a wannan zabe mai zuwa baya da bukatar kuri’ar su.

 • Sarkin Waka Naziru Ahmad ya ci Sarauta a Masarautar Kano

  Kamar yadda munka samo daga kundin Kannyood celebrities a wata kafar sada zumunta, Shahararren Mawakin Hausa Naziru Ahmad, wanda masoya ke kiraya da “Sarkin Waka” tun gabanin wannan ya samu sako daga fadar Masarautar Kano da sa hannun sarki za’a nada mai sarauta saboda irin gudummuwar da ya bada ga Sarki da Masarautar Kano baki dayanta. Sakon ga yadda yake rubuce ya nuna cewa:

  “Mai martaba ya umurce ni da na
  yi maka godiya bisa biyayya da
  soyayya da kake masa tun yana
  Dan Majen Kano har Allah ya sa
  ya zama Sarkin Kano wannan
  abin a yaba maka ne,” in ji
  Danburan a cikin takardar.
  Ya kara da cewa. “bisa haka mai
  martaba ya umurce ni da na
  sanar da kai cewa ya ba ka
  sarautar sarkin wakar sarkin
  Kano. Za’a yi nadin sarautar ran Alhamis 27 ga watan Disamba.

 • Jarumar Kannywood, Maryam Booth zata yi aure

  Tauraruwar yar wasa a Masana’antar Kannywood, Maryam Booth da Saurayin da zai aureta wani tauraron Mawakin Hausa wanda ya shahara, ance sun jima suna sheke soyayyarsu a boye kamar yadda munka samo, sun bayyana soyayyar tasu wadda zata kare da aure.

  Hotunan nasu sun bazu a kafofin sada zumunta Maryam Booth(Dijangala) wadda ta haskaka akwatunan kallonku tun tana yarinya karama da saurayinta mai suna Sadik Zazzabi. Sun yanke shawarar zama ango da amarya in mai kowa mai komi ya yarda. Allah yasa albarka Dijangala.

  Ga hotunan Maryam Booth masu kama da na kamin biki:


 • Music: Ado Gwanja- Labarin Soyayyar Gwanja da Maimuna

  Kwanakki mun kawo muku labarin soyayyar Mawakin mata Adamu Isah Gwanja da Matar da ya aura Maimunatu Hassan Kabeer, to wannan karon mun kawo muku labarin soyayyar tasu a waƙance, sauƙaƙe ba sai kun yi wahalar karantawa ba. Ko kun san mazaje nawa ya ba kanwa, ko kun san yadda ya tsallake anniyar yan bannar aure, ko kun san yadda ya kaya da yan suka- kafin ya mallaki wannan kyakkyawar yarinyar son kowa kin wanda ya rasa. Ku dauko wakar ku saurara ku ji!

  Download now
 • Lalata: An kama wani Magidanci dan shekara 48 tareda karamar yarinya

  Kamar yadda munka samo, an kama wani Magidanci dan shekara 48, Osei Maxwell, da hannu dumu-dumu yana aikata ta’asa a Legas bayan da makwabta sunka kamashi diyar makwabta yar shekaru 6 yana lalata da ita.

  Kafar P.M.EXPRESS ta bada rahoton cewa an kamashi hannu dumu dumu yana aikata laifin. Lamarin ya faru gidan Oke Idimu shiyar Idimu a Legas inda yake da zama. Makwabtan da sunka ji abunda ya faru sun yi ta mamaki yadda magidancin mai aure ya aikata wannan ta’asa ganin yana zamne tareda matarshi. Majiyar yan sanda tace Maxwell ya ja yarinyar karama zuwa dakinshi, ya tube mata wando sannan ya aikata wannan aika-aika.

  Kafin wannan,makwabtan da sunka ga alamun yadda yarinyar take kai-komo su sunka yi kokarin tura kofar dakin mutunen sunka ceto karamar yarinyar. An ce lokacinda aka tambayi yarinya abunda take yi tareda Maxwell ta bayyana cewa ya mata fyade. Uwayen ta sun kai kara hukumar yan sanda Ikotun Police Division; an kama mai laifin sannan aka tsare shi har sai yadda hali yayi. Yan sanda sun kama shi da laifi sun ka iza keyarshi

  Kotun
  Ogba Magistrates court da laifin lalata da kananan yara. Bayan zaman shari’a aka yi kurkuku dashi inda ya cigaba da zama kafin a yanke mai hukumci, ba biyan kudin fito.

 • Taron Nadin Sarautar Atiku Abubakar- Jiga-jigan Yan PDP sun hallara

  A ranar Lahadi ne aka yi Wankan Nadin Sarautar dan takarar Shugaban kasar Nijeriya, Atiku Abubakar a matsayin Wazirin Adamawa, inda yan siyasa da shugabannin da gwamnoni sunka hallara dan taya abokin aikin nasu murna ga samun wannan matsayin na Wazirin Adamawa. Cikin manyan baki akwai Chief Olusegun Obasanjo, Goodluck Ebele Jonathan, Senator Bukola Saraki, Ibrahim Badamasi Babangida, da dai sauransu.

  Atikun ya bayyana farin cikinshi cewa ba zai manta da wannan muhimmiyar ranar ba. Sannan kuma ya nuna farin cikinshi da halartar taron da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo yayi da sauran jigajigan shugabannin jam’iyar PDP.
Close

Adblock Detected

Please consider supporting us by disabling your ad blocker