Soyayya: Jarumin Kannywood, Adam A Zango yana sumbuntar matarshi yar Kamaru

0

Ummulkulsum kyakkyawar matar shahararren dan wasan Kannywood ce yar asalin kasar Kamaru wadda ya aura a shekarar 2015, itace cikon matan jarumin na ukku ko hudu duk da cewa ya taba sakin wasu a baya. Adam A. Zango ya watsa waɗannan hotunan ne tareda amaryar tashi suna sheƙe soyayya, harda sumbunta.

Prince Zango ya watsa hotunan ne a kundinshi na kafar sada zumunta, Instagram, wanda masoya dake bibiyarshi suka ta yabawa tareda masu addu’ar zaman lafiya.

Zango fitaccen jarumin Kannywood ne da ya sha karramawa da kyaututtuka daga kungiyoyin shirin kwaikwayo, saboda fitattun shirin da yake fitowa garesu da wanda yake shiryawa a masana’antar ta shirin kwaikwayo.

Leave A Reply

Your email address will not be published.