Labaran yau da kullum

Shugabannin darikar Tijjaniya sun kai ziyarar Barka da Sallah a Fadar Aso rock Abuja

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa shi fa na kowane yayinda yake karbar bakuncin yan darikar tijjaniya da suka kai mai ziyarar barka da sallah. A taron ya kara da cewa burin shi shine samarda cigaba mai dorewa ga yan Nijeriya.

Shugaban yayi wannan ikirarin ne a fadar Aso rock, jiya lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin darikar Tijjaniya a nahiyar Afrika karkashin jagorancin Sheikh Ahmed Tijjani Ibrahim Inyass dake zaman jika wurin Marigayi Sheikh Ibrahim Inyass.

Buhari ya godema dukkan ‘yan tijjaniyya dake a fadin duniya gameda irin goyon bayan da suke nuna mai da kuma fahimtar manufofin shi na alheri da suke.

Read also  Sojojin Nijar sun sake fatattakar Ƴan Bindigar Sokoto, sun kashe sama da 120
Tags

DanZubair

I am Abdul-Raheem Zubair by name, Founder- Operator at GobirMob.com. My hobbies are reading, travelling and discovering.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Close
Close
WhatsApp Join Group