Labaran yau da kullum

Sakamakon Fyade An yanke ma Wata Yar Pakistan Mummunan Hukumci Gaban ‘Yangidansu

Shin ka san adalci? Minene adalci? Shin adalci ne a hukumta wani a kan laifin wani? Labarin wani mummunan abu ne da ya faru a Kasar Pakistan, Kauyen Rajpur cikin garin Muzaffarabad dake Masarautar Punjab, inda an ka yanke ma wata budurwa hukumcin fyade gaban yan gidansu saboda ana zargin dan uwanta da aikata laifin fyade ga wata mata a garin nasu.

Abun dai shine Umar wanda ana zargin shi da yi ma yaruwar Ashfaq fyade a ranar 16 ga watan Juli inda abun ya kai ga kai kara wurin manyan gari, take babban shugaban garin ya yanke hukumcin cewa za’a yi ma diyar Umar mai kimanin shekaru 16 fyade a gaban yan gidansu inda Ashfaq ne da kan shi zai aikata fyaden dan rama ma yaruwar shi.

Read also  Cikakken Jawabin Shugaba Muhammadu Buhari na cikar Nijeriya shekaru 57 da samun yancin kai

Sai bayan yanke wannan kazamin hukumci da manyan gari sun ka kira da adalci dangi Umar wadanda sun ka daukaka ga yan sanda dan bima yar su hakkinta, hukumar yan sandar sun ka yi awon gaba da manyan garin su guda 30 hadi da Umar da kuma Ashfaq tareda daukar alkawarin tsaurara bincike da kuma kira ga Gwamnati dan a kara wayarda kan mutane kan cin mutumcin mata a duniya.

Hassan Haruna Gobir

Hassan Haruna Gobir, from Sabon Birni in Sokoto State, is GobirMob.com publisher and writer. He primarily focused on Nigeran politics, Gobir News and Sports.
Close
Close
WhatsApp Join Group