Labaran wasanni

Munyi nasara a komi kuma zamu cigaba da yin nasara- Perez

Real Madrid na cikin wani yanayi na koma baya a wannan kakar wasannin wanda hakan yasa suka kori kociyan su tun kafin tafiya tayi nisa wanda a yau manbobin kungiyar suka yi wani zama kafin wasan Real Madrid Da Real Valladollid inda taron ya samu halartar irin su Raul Gonzalez, Gento, Alvaro Arbeloa, Roberto Carlos da dai sauransu. inda shima shugaban kungiyar yake jawabi cewa kasancewa a wannan kungiya mai albarka yana nufin nuna kwazo da jajircewa hakika wannan kungiya tayi abun azo a gani domin shekarar data gabata mun lashe kofin zakarun turai suma mata sun lashe kofin wasan kwallon kwando wanda shine kofin zakarun turai na uku da muka lashe a jere kuma na hudu a cikin shekaru biyar wanda hakan yana nuni da cewa munyi nasara a komi kuma zamu ci gaba dayin nasara. daga karshe yayi jinjina ga mambobin kungiyar inda yayi jinjina garesu cewa lalle kun cancanci duk wani yabo domin duk nasarar da muka samu ba zata yiwuba idan baku domin kune kuka jure zama cikin nasara ko faduwa ba tare da ja da baya ba.

Tags

Hassan Haruna Gobir

Hassan Haruna Gobir, from Sabon Birni in Sokoto State, is GobirMob.com publisher and writer. He primarily focused on Nigeran politics, Gobir News and Sports.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Close

Adblock Detected

Please consider supporting us by disabling your ad blocker