Muna tareda ke Zainab Indomie- Adam A Zango

0

A kwanan nan tauraron Hausa films kuma mawakin Hausa hiphop, Adam A. Zango ya kaima Zainab Abubakar, tsohuwar jarumar Kannywood ziyara a madadin masana’antarsu ta Kannywood. Ga hoton ziyarar wanda ya hauda a kundinshi na kafar sada zumunta inda ya rubuta cewa, “Ina tare dake a ɗaukaka da rashinta.” Ya bayyana cewa yana tareda ita a daukaka da rashinta, cikin arziki da talauci, ya ƙara da cewa Allah yi miki Albarka Indo.

Zainab Indomie ta haskaka sosai a masana’antar kannywood amman sai aka bar jin labarinta da baya, an yita surutai iri-iri akan abunda ya sa aka bar jin duriyar tata ciki hadda wanda aka rinka cewa ciwon kanjamaune ya kamata.

Leave A Reply

Your email address will not be published.