Kundin Kannywood

Mun shirya Film din Rariya dan ya fadakarda Uwayen Yan jami’a, martanin Rahma Sadau ga Yar jarida

Wata yar jarida kuma tsohuwar ma’aikaciyar BBC Hausa, Kadaria Ahmed ta soki shirin nan da tauraruwar Kannywood Rahama Sadau ta shirya mai suna Rariya. Kadaria ta bayyana a kafar Instagram cewa a jiya ta ɗan kalli wani sashe na film din Rariya na tsawon mintuna ashirin kuma abunda ta fahimta shine, shirin zai iya sa iyaye su daina aika ‘ya’ya mata makarantun jami’a.

Kadaria ta kare zancenta da tambayar Rahama Sadau cewa, amman na tabbata ke ba abunda kike burin cimmawa kenan ba a wannan film din.

Rahama ta amsa mata da cewa, fatana shine shirin film din Rariya ya sa iyaye su kara saka ido akan ‘ya’yansu su kuma nuna musu sanin mutumcin kansu da darajar karatunsu fiye da rudin da wasu mutane ke musu da kayan alatu na karya. A karshe ta cewa kadaria da kin kalli film din har zuwa karshe da yafi.

Tags

DanZubair

I am Abdul-Raheem Zubair by name, Founder- Operator at GobirMob.com. My hobbies are reading, travelling and discovering.

You Might Like These:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Close

Adblock Detected

Please consider supporting us by disabling your ad blocker