Matsayin sunayen Hausawa na Gargajiya ga Hausawa

0

Harshen hausa ɗayane daga harsunan da aka fi amfani dasu a yankin Afruka, hannun riga da harshen Kiswahili da Larabci, kamar yadda ƙiyascin kwararru ya bada. Harshen ana amfani dashi yawanci a Afruka inda yakeda yawancin masu ji nai, kuma an ƙiyasto cewa mutanen sun kai kusan Miliyan 50. Harshen dangin harsunan Afruka da Asiya “Afro-asiantic language family” ya kuma kasance harshen cuɗanya ga yawancin kasashen Afruka k.m.r Arewacin Nijeriya, Jamhoriyar Nijar, Wasu ɓangarori cikin Kasar kamaru, Sudan, Libya, Cad da kuma tsakankanin Musulumin Gana, Gabon, Ibori Cos d.s.s. Yawancin hausawa dai sun bunzumane cikin Gusumci da Gabaccin Jamhoriyar Nijar, Arewancin Nijeriya, Sudan, Gana da Cad sannan kuma harshen ya kasance harshen kasuwanci ga wasu ƙasashen yamma ga Afruka k.m.r Binin, Gana, Kamaru, Togo, Ibori Cos d.s.s kasancewar yada zango da sunka yi can ta sanadiyar kasuwanci.

Bayan waɗannan abubuwan a zo a gani ko ci gaba, wasu ƴan suka ke gani ko tsammanin cewa hausawa basuda sunayen gargajiya ko kuma sun musanyasu da na larabawa da gangan, wanda haka ba gaskiya bace.

Hausawa kamar wasu Afrukawan, su ma sunada sunayensu na gargajiya nasu na kansu, wanda aka faro tun zamani mai tsawo dangane da gargajiyoyinsu da tunani irin nasu na zamantakewa.

Sunayen dai ana sawa jarirai ko mutane dai-dai lokacin haihuwarsu, yanayi haihuwarsu, jeri haihuwa cikin ɗaki, ko kuma aikin mutum cikin gari bayan ya girma. Mutum zai iya gane sunayen daga ambata, dan zurfafan kalamai na hausa da tunani irin nasu. Har wa yau rukunan Hausawa irinsu; Gobirawa, Tagamawa, Adarawa, Kurhwayawa, Cidarawa, Arawa, Daurawa, Kanawa, Kabawa, Katsinawa, Ranawa, Hadejawa, Zazzagawa da Zamfarawa na sa ma ɗiyansu sunayen tareda na larabawa ɗin. Kuma wasu daga cikin kabilu k.mBarebari (Kanuri), Yarabawa, Fulani, Azbinawa d.s.s da sunka zamna cikin Hausawa, su ma suna amfani da sunayen. Sarakunan Fulani na Sakkwato alal misali.

Babban dalilin da yassa Hausawa ke yawan sawa diyansu sunayen Larabci shine saboda wani hadisi kamar yadda Abu Dawud ya ruwaito.

“Sunan da za’a sama jariri ya kasance mai ma’ana, abin so da kauna. Ranar karshe, za’a kira mutum da sunanai da na uwayenai. Dan haka suna mai kyau ya zama dole. (Abu Dawud)”

Hausa na wancan zamanin na daure sun yi tarayya da Larabawa lokacin zamansu a Kasashen Larabawa, Gabas ta tsakkiya, sun yi auratayya dasu, sun ara musu gargajiyoyinsu da tabi’arsu kafin su baro yankin su koma yankin Afruka ta yanzu.

Sunaye irinsu Ibrahima(Abraham), Idirisa (David), Musa(Moses), Hajara, Safiya, Hasiya, Hana, Samu(Samuel, Shammil), Bilal, Balkisu, Yunusa, Isma’ila, Isiyaku, Yakubu. Yusufa(Joseph), Sulaimanu(Solomon) da sauran sunayen Annabawa da iyalansu nada ma’ana da hausa, tabakin manazarta harshen hausa. Haka wannan abun yake ga Sunayen Hausawa Kiristoci,kamar yadda Kiristocin Arewacin Nijeriya ke amfani dasu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.