Jarumar Kannywood, Fati Shu’umah tace bata ce tana son Shugaba Buhari da aure ba

0

Tauraruwar Kannywood, Fati Shu’uma ta fito ta ƙaryata wani labarin ƙamzon kurege da wata jarida ta yaɗa akanta, wai tace tana son Shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari da aure.
Jarumar tace tabbas tana son shugaba Buhari a matsayin shugaban al’umma na gari amman bada aure ba kuma bata yi hira da wata jarida ba kan haka, kamar yanda ake yadawa.

A wani gajeren bidiyo data wallafa a kundinta na Instagram, Fati tace wannan magana ƙagece kawai aka mata “Ƙaryace, Ƙaryace, Ƙaryace”, kuma tayi kira ga masoyanta da su watsa wannan dan karyata labarin dan wanketa daga zargin.

Leave A Reply

Your email address will not be published.