Labaran yau da kullum

Hotunan Malamar dake waƙiltar Nijar a Gasar Karatun Alkur’ani ta Duniya a Dubai

Kamar yanda mun ka samu daga sashen NijarHausa24 a Facebook ta hannun Ashirou Kornaka, waɗanda sun ka baza hotunan yarinyar mai shekaru ashirin da ukku (23) tana gudanarda nata karatun Alƙur’ani– zagaye na huɗu a haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Birnin Dubai. Ɗalibar mai suna Shafa’atou Issoufou Mouhmmadou ta ƙayatarda mutane sosai, inda ta sha ruwan addu’o’i da fata nagari daga mutanen kasar Nijar da makwabta, cewa Allah yasa ta ciwo ma Kasa Nijar matsayi na farko. Gasar musabakar karatun Alkƙur’anin ta duniya na gudana ne a halin yanzu a Birnin Dubai. Sannan kuma wasu masharhanta suna kyautata zaton ko diyar Shugaba Mouhammadou Issouhou ce, ganin sunayen mahaifinta ya zo daya da shi Shugabana Jamhoriyar Nijar din.

Read also  Jiya ba yau ba: Yadda Sir Ahmadu Bello da Sir Abubakar Tafawa Balewa ke Gudanarda Gangamin Neman Zabe

GobirMob na muku fatan alheri da nasara…

Tags

DanZubair

I am Abdul-Raheem Zubair by name, Founder- Operator at GobirMob.com. My hobbies are reading, travelling and discovering.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Close
Close
WhatsApp Join Group