Labaran yau da kullum

Hotuna: Yan China sun sha Wankan Rawunna ranar Nadin Sarauta a Kano

Jiya Alhamis ne aka yi taron wankan sarautar wani hamshaƙin dankasuwa daga Kasar China wanda munka baku labarinshi kwanakkin baya. Fadar masarautar ta kano ta yi wankan nadin sarautar ne a Fadar Masarautar Kano. An nada Mike Zhang a matsayin Wakilin ‘Yan Chanan Kano a Fadar Maimartaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu ranar Alhamis ɗin. Yan Kasar Sin mazamna Jahar Kano, abokan kasuwa dss sun halarci wannan taro inda har wanka sunka yo na rawunnan da dawakai don taya danuwan nasu murna. Zat kyawo, ba laifi.

Karshe Mike yayi jawabi cikin harshen Hausa cewa zai hada kan yan chanan kano don kawo cigaban kasuwanci a Jahar wadda tun da daɗewa take tafiyarda ragamar kasuwanci a Kasar Hausa da ma Nijeriya baki daya.

Read also  Amaryar Sarkin Ife tana share fagen zama Sarauniyar Masarautar Ile-Ife

Allah shi taya riko.

DanZubair

I am Abdul-Raheem Zubair by name, Founder- Operator at GobirMob.com. My hobbies are reading, travelling and discovering.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Close
Close
WhatsApp Join Group