Labaran yau da kullum

Hotuna: Sojojin Nijeriya sun kubtarda Shanu wajen Dubu daga Ƴan Bindiga

Hausawa sunce rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya ta mai kaya, wagga faɗar tayi daidai da matakinda Sojin sama na ƙasa wato Nigerian Air Force (NAF) ta ɗauka jiya kan ƴan bindigar Sabon Birni/Isa waɗanda sun ka jima suna gasama mutane aya ga hannu. Zamu iya cewa yanzu an fara samun galaba a kansu tun bayanda an ka tarwatsa mafakarsu ta Sabon Birni, tareda kubtarda shanu da yawansu ya kai kimanin ɗari bakwai (700), banda su Awaki, Tumaki da Raƙumai.

Tun tsawon watanni da dama yankin Sokoto-ta-gabas yake famada tashe-tashen hankula sanadiyar ƴan bindiga da sun ka samu gindin zama a wasu sassa na yankin, amman yanzu akwai fatan nasara sakamakon farmakinda Sojojin sama sun ka kai jiya Alhamis, 25 ga watan Yuli.

Read also  Hotuna: Zinder ta shirya tsab dan tarben Bikin 18 Decembre 2018

Ga hotunan shanun da an ka kubtar daga hannun ƴan ta’addan:

DanZubair

I am Abdul-Raheem Zubair by name, Founder- Operator at GobirMob.com. My hobbies are reading, travelling and discovering.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Close
Close
WhatsApp Join Group