Labaran yau da kullum

Dan kabilanci ne- Fadar Shugaban kasa ta bankado yadda Peter Obi ya koro Yan Arewa

Fadar Shugaban kasa ta goyi bayan Gwamnan Kaduna Malam Nasiru El-Rufai ga kiran Tsohon Gwamnan Jahar Anambra Mr Peter Obi dan kabilanci, wato Mataimakin dan takarar Shugaban kasa Atiku Abubakar karkashin jam’iyar PDP. Malam El-Rufai a wani sako da ya saki a kafar Twitter ya kirayi Obi da wannan kalmar yace shi yasa hukumar DSS ta kameshi a shekarar 2014, shi Obi ya furta cewa “El-Rufai baida wani aikin zama a Jahar Anambra dan ba Jahar Katsina bace.”

Karawa da karau, wani na hannun daman
Shugaba Buhari, Bashir Ahmad, a sakon da ya aika a kundinshi na Twitter shima, ya kara ma Obi laifi dan ya taba koro Yan Arewa daga Jaharshi lokacin yana Gwamna. Maida martani ga sakon Peter Obi,
Ahmad ya rubuta cewa: “Lokacin kana Gwamna ka koro Yan Arewa suka komo gida, yawancinsu daga Jahata, Kano,
Jigawa, Katsina dss, kuma har yanzu basu mance da wannan wulakancin ba. Bama su bukatar ayi musu tuni. “Abunda Mallam El-Rufai yayi tunatarwa ne, amman su wadannan mutanen basu manta ba ko kusa, da yawa daga cikinsu sun rasa ayukkansu da kasuwancinsu. Tabbas, zasu rama a watan Fabrairu 2019, zabe mai zuwa.”

Tags

DanZubair

I am Abdul-Raheem Zubair by name, Founder- Operator at GobirMob.com. My hobbies are reading, travelling and discovering.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Close

Adblock Detected

Please consider supporting us by disabling your ad blocker