Labaran yau da kullum

Abunda yassa nake girmama Buhari:- Wani Gwamnan PDP

Wani Gwamna da aka zaba a karkashin Jam’iyar adawa ta PDP ya bayyana dalilin da yassa yake girmama shugaba Muhammadu Buhari duk da bambancin jam’iyar dake tsakani.

Gwamnan dai na Jahar David Umahi yace yana matukar girmama shugaban ne saboda alakar dake tsakanin su.

Mr Umahi dai shine kadai gwamnan daya fito daga kudu maso gabas dake da wata jituwa tsakaninshi da Shugaba Buhari wanda ko a can baya sai da ya fito fili ya bayyana cewa lalle shi zai goyama Buhari baya a zabe mai zuwa tun kafin ma shugaban ya bayyana anniyarshi ta tsayawa takarar shugabancin kasa a karo na biyu, zaben da za’a gudanar a watan yau.

Read also  Tarihin Margyayiya Hajiya Binta Kofar Soro wadda ta rigya mu gidan gaskiya

Gwamnan dai ya kara da jan hankalin cewa mutane su guji kwatanta dangantakar su da yima jam’iya zagon kasa inda yake cewa tun daga farkon lokaci Jahar Ebonyi PDP ce kuma har yanzu tana hannun ta don haka kada wani ya shiga tsakanin alaka ta da Shugaban kasa don wannan tsakanin mu ne kada a sanyashi a siyasa.

Hassan Haruna Gobir

Hassan Haruna Gobir, from Sabon Birni in Sokoto State, is GobirMob.com publisher and writer. He primarily focused on Nigeran politics, Gobir News and Sports.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Close
Close
WhatsApp Join Group