Abubuwan ban Mamaki 15 da baku sani ba gameda Rakumai

0

Wasu mutane na yawancin danganka rakumai da hamadar Gabas ta tsakkiya, duk da cewa akwai miliyoyin waɗannan bisashen masu tozo a yankin Afruka. Ana samun yawancinsu a Kasashen Afrika – cikin Masar da Moroko dakeda iyaka da Hamadar Sahara; ko cikin Kasashen Afrika da ake kira “Horn of Africa” kamar Ethiopia da Djibouti. Cikin Yankin Afrika ta yamma ana samunsu a ƙasashe irinsun Jamhoriyar Nijar, Mali da Nijeriya.

Akwai ire-iren Rakumai kashi biyu:
Rakuman Dromedary ko Rakuman Larabawa: masu tozo guda da Rakuman Bactrian. Waɗannan ire-iren Rakuman gida biyu ana samunsu a yankuna dabam-dabam a faɗin duniya. Rakuman Dromedary: Ana kiransu kuma Rakuman Larabawa, su ana samunsu a Arewaci, Yammaci da Gabas ta tsakkiya, wadannan irin tozo guda kaɗai ke garesu. Rakuman Bactrian: Waɗannan ana samunsu a yankin Asiya ta tsakkiya, waɗannan sun sha bam-bam da na farkon; sune Rakumai masu tozo guda biyu, sunada yawancin gashi a jikinsu saboda yanayin mazamninsu kuma an fi amfani dasu ga ci da sarrafa gashinsu in aka keɓe na farkon. Ba tareda bambatawa ba, Rakumai ana samunsu a hamada. Amman mutane na ganin cewa Rakumai na zama a wurare masu zafi, suna yi a kasashen masu sanyi. Ga jerin “Abubuwan ban mamaki 15 da baku sani ba gameda Rakumai.”

1. Raƙumai nada kaifin ƙwaƙwalwa fiyeda kowace dabba a duniyar dabbobi. Sunada yawan tunani kuma suna tunowa da komi. Idan mutum ya ɓatama Raƙumi ba zai taɓa mancewa ba kuma zai yi duk mai yuwuwa yaga ya kama mutum. Kuma in rana ta ɓace, in ba’a yi sa’a ba, zai iya kashe mutumin. Sunada ganewa, suna ƙyale yara ƙanana idan suka taƙulesu, amman sukan gwammace ramawa idan manyane dan suna ɗaukar abun kamar reni.

2. Rakumai dabbobine masu kyautaya zamantakewa tsakaninsu, suna yin gungu gungu da babban jagoransu Amale, inda kuma ƙananan Rakumai ke nasu gungu na dabam. Rakumai na kyautata zamntakewa matuƙa kuma suna gaisuwa tsakaninsu ta hanyar hurji ga fuskoki yanuwansu.

3. Rakumai na iya gudun da yakkai nisan kilo 40 cikin sa’i guda sanda ubangidajensu ke cikin sauri ko a’a.

4. Ana alaƙanta Rakumai da cewar baiwa daga Allah dan saboda rawar da suka taka a da lokacin daure da aka sha yake-yake.

5. An san Rakumai da tofama mutane miyau. A gaskiya, suna fitarda abincin dake cikin cikinsu tareda miya ɗin. Wannan hanyar kariyace in anka ɓata musu rai.

6. Rakumai nada jerin gira biyu masu kabrin gaske dake kare idanuwansu daga ƙurar Hamada. Suna kuma iya daɗe hantunansu da laɓɓansu dan fitarda ƙurar.

7. Rakumai na iya cin kusan komi mai ciyuwa ba tareda sun jima bakunansu ba, harda ƙayoyi da ƙaimu. Bisashene masu cin haki, kenan, ba zaku taɓa ganinsu suna cin nama ba.

8. Fitsarin Rakumai kabri gareshi kamar madara dan suna adana ruwa. Da kashinsu da fitsarinsu duk ana amfani dashi wajen magani.

9. Nononsu wanda yakeda ƙamshin itatuwa, yanada amfani ga lafiyar jikin mutane, yana tattareda yawancin sinadarin dake tabbatarda lafiyar jiki, kyawon jiki, kuma yanada ƙaramcin kitse. Yana taimakawa waken kare lafiyar mutum, tabbatarda gudanar jini, tabbatarda girma, maganin cutar zaki (diabitis) d.s.s

10. Tozon Rakumi ba ma’adanar ruwa bace kamar yadda mutane ke zato. Duk da cewa suna zama a wurare masu yanayin zafi, tozonsu na adana kitse kuma yana taimakama jikinsu ya sanyaya. In suna bukata, kitsen na zamewa abinci da ruwa dan amfani garesu.

11. In Rakumi ya kusanta ga ruwa, yana shan ruwa da sauri, yakan sha adadin da yakkai jarka 30 cikin mintuna 13. Jikin Rakumi na shan ruwa fiyeda na kowace dabba a doron kasa.

12. Uwa Rakuma na ɗaukar cikin Jaririn Rakumi tsawon kimanin watanni sha-hudu (14) kafin ta haihu.

13. Bayan waɗannan abubuwan ban mamaki da ban al’ajabi da Allah ya huwacema Ramumakai dashi, Ubangiji cikin nashi iko na dabam ya ƙaddaro musu tsoron Kunama. Da hango ƙanƙanuwar Kunama daga nesa, Makeken Rakumi zai nemi hanyar mafita dan harbin kunawa garesu mutuwa ce dan takunansu tabshi garesu kamar kaɗa.

14. Rakumai bisashe ne wanda aka sha jigila dasu a Hamadar Sahara: Misali da Abzinawan Agadez a Jamhoriyar Nijar.

15. Da ƙarshe, A cikin Alkur’ani mai tsaki an ambaci halittarsu mai ban mamaki a wata aya, “Basu ga Rakumai ba, yadda aka haliccesu?― Da kuma sararin samaniya, yadda aka ɗagata sama? Da tsaunukka yadda aka kakkafasu?― Da doron kasa, yadda aka shimfidata?”
(al-Ghashiya, 17-20)

Leave A Reply

Your email address will not be published.